Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana shirye-shiryen kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a ƙasashen Isra’ila da Iran.
Wannan mataki na zuwa ne bayan ɓarkewar sabon rikici tsakanin ƙasashen biyu.
- An Ɗaure Wani Mutum Wata 6 Kan Satar Takalma A Masallaci A Kaduna
- Wani Matashi Ya Ƙone Kansa A Kano Saboda Yana Son Zuwa Aljanna
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a daren Talata, an bayyana cewa ofisoshin jakadancin Nijeriya a Tel Aviv (Isra’ila) da Tehran (Iran) na ƙoƙarin tuntuɓar ‘yan Nijeriya domin tabbatar da dawowar su cikin aminci.
An shawarci duk ‘yan Nijeriya da ke waɗannan ƙasashe da su kiyaye dokoki da matakan tsaro na cikin gida, tare da tuntuɓar ofishin jakadancin Nijeriya mafi kusa domin yin rijista da samun ƙarin bayani.
Ma’aikatar ta yaba da jajircewar ma’aikatan jakadancin Nijeriya a ƙasashen biyu, tare da tabbatar da cewa gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin kare lafiyar ‘yan Nijeriya a ƙasashen waje.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro.
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a waɗannan ƙasashe.
“Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntuɓar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun ƙarin umarni.”
Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da faɗa tsakanin Isra’ila da Iran, tare da buƙatar ɓangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci.
Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar lumana da kuma tallafa wa zaman lafiya a yankuna da duniya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp