• English
  • Business News
Sunday, June 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hikimar Yunƙurin Sake Farfaɗo Da Noman Filanten A Jihar Nasarawa

by Abubakar Abba
9 hours ago
in Noma Da Kiwo
0
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ci gaba da yunkurin farfado da noman Filanten kimanin Kadada 6.5 a Jihar Nasarawa, wani kamfanin gidan gona mai suna ‘AA Dibine Agro’ da wata kungiyar manoma (COMAFAS), sun rattaba hannu tare kulla yarjejeniya; domin ci gaba da noman Filanten a fadin Jihar.

Isiaka Adamu Adamu, Manajan Darakta na Kamfanin ‘AA Dibine Agro Farm Limited’ da Dakta  Austine Maduka, wanda ya kafa kungiyar ta ‘COMAFAS’, sun amince da yarjejeniyar hadin gwiwar a lokacin da suka ziyarci gonar, don kulla dangantakar.

  • Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
  • Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa

Sun sanar da amincewar ne, a lokacin da suka kai ziyara kamfanin, inda a hukumance suka aminta da dangantar da kuma hadakar tasu.

Wannan yarjejeniyar ta kasance a matsayin wani babban mataki na kara bunkasa noman na gonar, duba da irin dimbin albarkatun da ake da su, duk da cewa ana fuskantar karancin kudaden aiki, domin samar da kayan aikin da suka kamata da za a yi amfani da su wajen yin noman a gonar.

Dakta Maduka ya bayyana cewa, za kuma a samar da wasu karin wasu dabarun zamanin da za a yi aikin da su a gonar.

Labarai Masu Nasaba

Jigawa Za Ta Samar Da Kashi 25 Na Shinkafar Da Nijeriya Ke Bukata – Hon Abdurahman 

Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 

Gonar ta ‘AA Dibine Agro’, ta kasance a yankin Pasali Karshi da ke cikin karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.

Kazalika, kudirin shi ne; nomawa da kuma samar da isasshen Filanten din da za a rika kai wa har zuwa babban birnin tarayya  Abuja, domin sayar da shi.

A cewar tasa, abin da gonar ke son cimma shi ne, taimaka wa fannin aikin noma na tarayyar kasar nan, wanda hakan zai kuma kara tallafawa wajen kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa tare da samar da wadataccen abinci.

Sai dai, ya bayyana cewa; rashin kudaden da za a yi amfani da su wajen cimma wannan manufa, su ne babban cikas.

Gonar, wadda aka samar da ita a zagayen Katangu, domin kiwon dabbobi, na matukar fama da karancin ruwa da ya yi sanadiyyar dakatar da gudanar da dukkanin wasu ayyuka da ake yi a cikinta.

Bugu da kari, rashin samar da hanya; wadda za a rika amfani da ita wajen safarar amfanin gonar da aka girbe, na daya daga cikin kalubalen da gonar ke fuskanta.

Amma duk da irin wadannan matsaloli da gonar ta ‘AA Dibine’ ke fuskanta, ta tanadi wasu muhimman manya-manyan shirye-shiye.

Daga cikin shirye-shiyen sun hada da; burin samar da wuraren kiwon dabbobi da kiwon Kajin gidan gona da wuraren kiwon Kifi da kuma sarrafa abincin dabbobi, wanda hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da ayyukan yi da kuma kara bunkasa noma.

kungiyar ta COMAFAS, ta fi mayar da hankali ne wajen tallafa wa manoma da kuma kara habaka fannin aikin noma.

A cewar Dakta Maduka, kungiyar ta amince da yarjejeniyar ce, duba da cewa; ta lura da manufar da gonar ta ‘AA Dibine Farm Limited’, ta sanya a gaba, musamman domin tsamo gonar daga cikin babban kalubalen da take fuskanta tare kuma da samun damar cimma burin da ta sanya a gaba.

Ya kara da cewa, hadakar za kuma ta taimaka wajen samar da ilimi da masu zuba hannun jari da kuma samun tallafin kudi ga gonar. Haka zalika, kudin zai taimaka, wajen sama wa gonar kayan aikin da take bukata da kuma samar da hanyar yin jigilar amfanin gonar da aka shuka.

Sauran daukin da hadakar za ta samar, sun hada da horo da kuma tabbatar da shugabanci nagari da sauran makamantansu.

Dakta Maduka, ya kuma bayar ta tabbacin cewa; ta hanyar jawo sauran abokan hadaka cikin wannan aiki, za a iya noman wannan Filanten mai matukar tarin yawa a gonar, duba da cewa; yankin na da yanayi mai kyau na yin noma da ake bukata, inda kuma hakan zai kara taimakawa wajen samar da ayyukan yi.

Kazalika, ya bayyana cewa; hadakar za kuma ta kara taimakawa wajen kara habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da wadataccen abinci yadda ya kamata. 

A cewar tasa, gonar ta ‘AA Dibine Farm Limited’, za ta kasance mai aiki da kayan noma na zamani a tsakanin sauran gonakin da ke fadin kasar nan, ta hanyar taimakon kungiyar ta COMAFAS.

Har ila yau, daukacin masu kulla wannan yarjejeniya, sun amince da kara habaka wannan bangare na noma a dukkanin fadin Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AyabaFilantenPlantain
ShareTweetSendShare
Previous Post

Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?

Next Post

Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman – Iran

Related

Jigawa Za Ta Samar Da Kashi 25 Na Shinkafar Da Nijeriya Ke Bukata – Hon Abdurahman 
Noma Da Kiwo

Jigawa Za Ta Samar Da Kashi 25 Na Shinkafar Da Nijeriya Ke Bukata – Hon Abdurahman 

1 day ago
Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 
Noma Da Kiwo

Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 

2 days ago
Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA
Noma Da Kiwo

Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA

1 week ago
Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025
Noma Da Kiwo

Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025

1 week ago
Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

2 weeks ago
Neja
Noma Da Kiwo

Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja

2 weeks ago
Next Post
Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman – Iran

Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman - Iran

LABARAI MASU NASABA

Mun Gano Wurare 52 Da Ake Aikata Laifuka A Kano – Janar Mai Adda’u

Mun Gano Wurare 52 Da Ake Aikata Laifuka A Kano – Janar Mai Adda’u

June 22, 2025
Me Ya Sa Kamfanonin Kasa Da Kasa Ke Da Imanin Gudanar Da Harkokinsu A Kasar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Kasa Da Kasa Ke Da Imanin Gudanar Da Harkokinsu A Kasar Sin?

June 22, 2025
Rashford Na Fatan Buga Ƙwallo Tare Da Lamine Yamal A Barcelona

Rashford Na Fatan Buga Ƙwallo Tare Da Lamine Yamal A Barcelona

June 22, 2025
Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Bam A Borno, Ya Yi Alhinin Fashewar Wani A Kano

Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Bam A Borno, Ya Yi Alhinin Fashewar Wani A Kano

June 22, 2025
Gwamnatin Hong Kong Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru Biyar Da Kafuwar Dokar Tsaron Kasa Ta Yankin

Gwamnatin Hong Kong Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru Biyar Da Kafuwar Dokar Tsaron Kasa Ta Yankin

June 22, 2025
Barayin Wayar Lantarki Sun Addabi A’lummar Jihar Kebbi

Barayin Wayar Lantarki Sun Addabi A’lummar Jihar Kebbi

June 22, 2025
Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran

Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran

June 22, 2025
Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

June 22, 2025
Bernado Silba Ya Zama Sabon Kyaftin Din Manchester City 

Bernado Silba Ya Zama Sabon Kyaftin Din Manchester City 

June 22, 2025
Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman – Iran

Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman – Iran

June 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.