ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman – Iran

Iran ta murza gashin baki kan Amurka

by Sulaiman
1 year ago
Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, jiragen yakin Amurka B-52 sun yi nasarar jefa bama-bamai a tashoshin nukiliyar Iran a Fordo, Natanz, da Isfahan, wanda Isra’ila tasha alwashin kawo karshen shirin nukiliyar kasar.

 

Harin bama-bamai na Amurka ya kara ta’azzara rikicin da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Iran wanda ya shiga kwanaki 10.

ADVERTISEMENT
  • Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?
  • Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi

A cikin wani jawabi na kasa daga Fadar White House, Shugaba Trump ya gargadi Iran kan tunanin ramuwar gayya, inda ya ce, hari mafi girma na jiranta.

 

LABARAI MASU NASABA

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.

 

Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”.

 

Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

 

Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani a wuraren, kuma dama tun kafin harin, an riga an kwashe duk wasu abubuwa masu muhimmanci na tashoshin nukiliyar”.

 

Tun da farko, Tehran ta yi gargadin cewa za ta kai hari kan muradun Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya domin daukar fansa kan duk wani hari da Amurka ta kai, kuma ya zuwa yanzu ta harba makamai masu linzami kan Isra’ila, inda aka ji karar fashewar wasu abubuwa a birnin Kudus.

 

A halin da ake ciki, kawunan ‘yan majalisar dokokin Amurka ya rabu dangane da shigar kasar, inda ‘yan jam’iyyar Republican suka yabawa Trump, yayin da ‘yan jam’iyyar Democrat suka yi gargadin cewa an jefa Amurka cikin wani yakin da ba nata ba.

Amurka
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

MASU ALAKA

Amurka
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Amurka
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Amurka
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Next Post
Bernado Silba Ya Zama Sabon Kyaftin Din Manchester City 

Bernado Silba Ya Zama Sabon Kyaftin Din Manchester City 

LABARAI MASU NASABA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Amurka

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Amurka

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Amurka

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.