Ya zuwa ranar Lahadi, madatsar ruwa ta kogin Yangtze ta saki ruwan da ya kai kyubik mita miliyan 980 cikin sashen kasa na kogin, a matsayin mataki na rage tasirin fari dake addabar wasu yankunan kudancin kasar Sin.
Kafar CMG ta hakaito ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasar Sin na bayyana cewa, sakin ruwan bangare ne na shirin shigar da jimillar ruwa da yawansa ya kai kyubik mita biliyan 1.48, cikin sashen kasa na kogin Yangtze.
Tun daga watan Yuli, sassan yankunan kogin Yangtze da dama na fuskantar karuwar yanayin zafi, tare da raguwar kaso 45 bisa dari na ruwan sama, idan an kwatanta da shekarun baya.
Ma’aikatar ta ce, tsakanin ranakun 1 zuwa 15 ga watan nan na Agusta. Madatsan ruwa ta kogin Yangtze sun tura adadin ruwa har kyubik mita biliyan 5.3 zuwa yankunan tsakiya da na kasan kogin.
Ya zuwa yanzu, fari ya shafi mutane miliyan 2.46, ya kuma mamaye fadin filayen noma kimanin hekta miliyan 2.2 a lardunan Sichuan, da Hubei, da Hunan, da Jiangxi da Anhui da birnin Chongqing.
A cewar ma’aikatun kudi da na ayyukan gaggawa, zuwa ranar 18 ga watan Agustan nan, an ware jimillar kudi har yuan biliyan 1.35, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 198, domin ayyukan shawo kan kalubalen ambaliyar ruwa da fari, a yankunan da ke fuskantar wadannan matsaloli. (Saminu Alhassan)