Wani jigo a jam’iyyar APC, Eze Chukwuemeka Eze, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ka da ya sake neman wa’adin mulki na biyu a shekarar 2027.
Eze ya yaba wa fitattun ’yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Chibuike Amaechi, da Nasiru El-Rufai saboda kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna All Democratic Alliance (ADA).
- Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin
- Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya
A cikin wata sanarwa da ya fitar daga birnin Fatakwal, Eze ya soki gwamnatin Tinubu, yana cewa ta gaza ƙwarai a cikin shekaru biyu da suka wuce.
Ya ce mulkin Tinubu ya jawo wa Nijeriya koma baya sosai a fannin dimokuraɗiyya da tattalin arziƙi.
Ya ce, “Lokaci ya yi da Shugaba Tinubu zai fara shirin komawa gidansa a Bourdillon, domin mulkinsa ya jawo wa Nijeriya azaba, cin hanci, rashin iya shugabanci da nuna bambanci.”
Eze ya gode wa waɗanda suka kafa ADA saboda ƙoƙarinsu na ceton Nijeriya daga hannun shugabannin da ba sa bin tsarin dimokuraɗiyya.
Ya ce sun nuna ƙwazo da ƙaunar ƙasa.
Ya ce, “Kun nuna bajinta da kishin ƙasa ta hanyar ƙoƙarin ƙwato mulki daga hannun shugabannin da suka haddasa rikice-rikice, garkuwa da mutane, talauci, yunwa da kunya ga ƙasar nan.”
Eze ya kuma yi addu’ar cewa Allah Ya taimaka musu su samu nasarar ceto Nijeriya daga hannun shugabanni marasa ƙwarewa da tausayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp