Ana kyautata zaton ‘yan bindiga da sojoji da dama sun mutu a wata musayar wuta da aka yi ranar Talata a Kwanan-Dutse da ke karamar hukumar Mariga a jihar Neja.
An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki ne a sansanin sojoji dake Kwanan-Dutse mai tazarar kilomita kadan da Bangi, hedikwatar karamar hukumar Mariga.
- Tinubu Zai Rattaba Hannu Kan Kudirorin Sauya Fasalin Haraji 4 A Yau Alhamis
- Sin Ta Sha Alwashin Rarraba Fasahohinta Na Ainihi Da Dabarunta Na Kirkire-Kirkire Tare Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa
A jiya ne rundunar sojin kasar ta tabbatar da mutuwar sojoji 17 tare da jikkata wasu da dama a lamarin, ko da yake mazauna yankin sun ce adadin na iya fin hakan.
Majiyoyi sun kuma ce “an kashe adadi mai yawa na ‘yan bindigar”.
Shugaban karamar hukumar, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya ce harin ya kara firgitar da manoman yankin.
Ya ce taimakon gaggawa daga barikin soji na Kontagora ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa zuwa dazuka.
Ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu, sun farfasa shaguna tare da kwashe kayan abinci da kayayyaki masu daraja a shagunan mutanen yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp