• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yajin Aikin ASUU: Malamin Jami’a Ya Yi Barazanar Ajiye Aiki Kan Rashin Albashi

by Najib Sani
3 years ago
Dakta Auwal Mustapha Imam

Dakta Auwal Mustapha Imam

Wani malami a  Jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi, Dakta Auwal Mustapha Imam, ya yi barazanar ajiye aikinsa matukar gwamnati ta ki biyan malamai albashinsu na watanni da suke bi tun bayan tsunduma yajin aikin ASUU.

Ya bayyana hakan ne a hirarsa da LEADERSHIP Hausa, Inda ya ce shi ne kadai malamin da yake da digiri uku a duk tsangayar, inda ya sha alwashin barin aiki a Jami’ar matukar ba a biya shi albashinsa na watannin baya ba.

  • Zan Mayar Da Jami’o’i Karkashin Kulawar Gwamnatocin Jihohi Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku
  •  ‘Yan Daba Sun Tarwatsa Taron Gangamin Takarar Atiku A Ribas

A cewarsa, malamai masu yajin aikin sun cancanci a biya su albashinsu na watannin da suke yajin aiki, inda ya yi ikirarin cewa duk da sun rufe azuzuwa amma suna yin bincike na ilimi da kuma duba kundin daliban da ke shirin kammala digiri saboda haka sun cancanci a basu albashi.

Ya ayyana matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na kin biyansu albashi don sun tafi yajin aiki a matsayin mugunta.

“An saka mu cikin wahala da gangan, muna cikin talauci. Mutane na cikin bashi da matsaloli iri-iri. Akwai wadanda a cikinmu motar haya suka koma tukawa, wasu sun sayar da motocinsu. Rashin kyautawa ne, zalunci ne gwamnati ta ce ba zata ba da wannan kudin ba” Inji shi.

LABARAI MASU NASABA

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Malamin ya ci gaba da cewa akwai ire-irensa da yawa da zasu bar aikin, su nemi wasu wuraren da za a mutunta su muddin aka ki biyansu albashin watannin baya.

Imam ya jaddada cewa sun tafi yajin aikin ne domin kubutar da ilimin jami’oi kada ta lalace kamar yadda gwamnati ta lalata makarantun firamare da sakandare a cewarsa.

Babban malamin, ya ce daya daga cikin abubuwan da suke bukata daga gwamnati shi ne a ba jami’oi damar yin amfani da kudadensu na shiga.

Ya ce jami’oi suna amfani da kudadensu wajen biyan wasu malamai daga wasu wurare saboda karancin malaman jami’a a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa muddin ba a ba su ‘yancin cin gashin kansu ba game da kudadensu, to, ba za su iya daukar malaman haya ba don cike gurbin rashin isassun malamai na dindindin a makarantunsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 
Manyan Labarai

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
Manyan Labarai

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Next Post
Sin Za Ta Jagoranci Samar Da Kundin Tsarin Amfani Da Sabbin Makamashin Samar Da Lantarki Na Farko A Duniya

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

October 30, 2025
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

October 30, 2025
Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

October 30, 2025
ASUU

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.