Kasar Zambiya ta kaddamar da tashar samar da wutar lantarki ta makamashin hasken rana mai karfin megawatt 100, wadda ta zama tashar lantarkin hasken rana mafi girma da aka taba samarwa a kasar zuwa yau, lamarin da ke nuna muhimmin ci gaban da aka samu wajen cike gibin karancin makamashi da kasar ke fafutukar yi.
Tashar, wadda kamfanin PowerChina na kasar Sin ya gina, tare da gudanar da aikin injiniya, da sayen kayayyaki da kwangilar gine-gine, an samar da ita ce a gundumar Chisamba ta tsakiyar Zambiya.
- Me Ya Sa JKS Mai Tsawon Tarihin Sama Da Shekaru 100 Ta Dore A Kan Mulki
- Xi Ya Bukaci Kungiyoyin Matasa Da Dalibai Su Zurfafa Gyare-Gyare Da Kirkire-Kirkire Don Samun Sabbin Nasarori
Bikin kaddamar da aikin ya samu halartar shugaban kasa Hakainde Hichilema, da jami’an gwamnati, da wakilan ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar ta Zambiya, da kuma manyan jami’ai daga kamfanin PowerChina.
Da yake jawabi, Hichilema ya yaba wa kamfanin na kasar Sin bisa hadin gwiwar da ya yi a wannan aikin, yana mai cewa, kawancen ya nuna yadda ake habaka hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa harkokin kasuwanci da cudanya a tsakanin jama’a.
A nata bangaren, mai ba da shawara a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Wang Li, ta bayyana cewa, “Hadin gwiwa a fannin makamashi wani bangare ne na zumunci mai fadi da ke tsakanin kasashen biyu.” inda ta kara da cewa, kasar Sin na ci gaba da ba da goyon baya ga kasar Zambia wajen cimma burinta na samar da makamashin hasken rana mai karfin megawatt 1,000. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp