Tsohon golan Nijeriya Peter Rufai, ya rasu yana da shekaru 61 a duniya. Rahotanni daga Radio Nigeria sun tabbatar da cewa Rufai ya rasu ne a ranar Alhamis, 3 ga Yuli, 2025, bayan fama da jinya ta dogon lokaci da ta sa ya janye daga harka ta jama’a.
A halin da ake ciki, dangin marigayin da kuma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ba su fitar da sanarwa a hukumance ba dangane da rasuwar tasa ba. Sai dai labarin mutuwarsa ya fara yaɗuwa a kafafen watsa labarai da kuma tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni.
- Kaftin Din Super Eagles, Ahmed Musa Ya Bukaci A Gaggauta Kawo Karshen Kashe-kashen Rayuka A Benuwe
- Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149
Peter Rufai yana daga cikin shahararrun masu tsaron Ragar Super Eagles da suka taka rawar gani a fagen ƙwallon ƙafa. Ya buga wa Nijeriya wasanni 65, ciki har da halartar gasar cin kofin duniya sau biyu da kuma taimakonsa wajen lashe kofin nahiyar Afrika (AFCON) a shekarar 1994.
Rasuwar Rufai za ta bar babban giɓi a zuciyar masoya wasan ƙwallon ƙafa a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya, duba da irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban wasan a ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp