Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine.
Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin. An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan.
- CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari
- Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
Majiyar ta ce haɗin gwuiwar jami’an Soja, da ‘yansanda, da masu farauta da ‘yan bijilanti sun bi sawun maharan cikin dazuka, lamarin da ya tilasta su bar ɗan ƙasar China da suka sace. “Har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a dazukan yankin don kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika,” in ji ta.
Kakakin Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya ce yana jiran cikakken rahoto daga DPO na yankin kafin ya bayar da ƙarin bayani. Majiyar ta kuma buƙaci a ƙara yawan jami’an tsaro a yankin da sauranɓm ɓɓ wuraren da ake fargabar barazanar tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp