Kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 88, da dukkan al’ummar kasar ta fara yakin kin jinin harin sojojin Japan a yau Litinin. Inda a wani bangare na bikin aka kaddamar da wani baje koli mai taken “Domin ‘yantar da kasa da zaman lafiyar duniya”.
An gudanar da bikin tare da baje kolin ne a babban dakin adana kayayyakin tarihi masu nasaba da yakin, wanda ke kusa da gadar Lugou, wadda kuma ake kira da “Marco Polo Bridge”, wurin da sojojin Japan suka fara kaiwa sojojin kasar Sin hari a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937, lamarin da ya zamo tushen mamayar da sojojin na Japan suka yiwa kasar Sin.
Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma sakataren sakatariyar JKS Cai Qi, ya gabatar da jawabi yayin taron, inda ya kuma ayyana bude baje kolin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp