Asibitin Kwararru na Best Choice ya sake bijiro da wasu ayyukan farantawa al’umma bayan bude fayil kyauta da rage kaso 50% cikin ayyukansu da suka fara a satin da ya gabata.
Yanzu haka asibitin ya sake tanadar kwararrun likitoci masu yin wadannan Tiyatar
( Urology) Aikin Mafitsara
(Hynea) Qabar ciki
(Orthopaedic) Aikin Qashi,
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne
(Dental) Hakori
(Fibroid) Qarin mahaifa,
(Urology) Aikin Mafitsara
Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya.
- Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu
- Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba
Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar LEADERSHIP HAUSA a ranar Litinin.
Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga kuma yawan da mutane suka yiwa gwamnati shi yasa hukumar gudanarwar Asibitin Kwararru na Best Choice itama taga da cewar bada tata gudummawar domin kara karfafar gwamnati a wannan fannin.
Auwal ya kuma bayyana jin dadinsa ganin yadda al’umma suke ta cin gajiyar bude fiyil kyauta da rage kaso 50% ganin likita tare da manya da kananan ayyukan asibitin da yayi a satin da ya gabata.
Dukkannin waɗannan ayyuka za a fara gudanar da sune a yau Litinin, don haka ga masu irin wadannan matsaloli za su iya zuwa domin a tantancesu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp