Wani taron sirri kan makomar siyasar Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya jefa jam’iyyar PDP cikin fargaba.
Wata majiya daga kungiyar yakin neman zaben Tinubu, ta shaida cewa, taron wanda ya samu halartar mutane biyu daga kowanne bangare ya yi albarka.
- Tilas Ne Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Mataki Kan Kisa Sheikh Aisami – Sheikh Bala Lau
- “Ɗaukar Abdulkarim Daura Matsayin Mataimakin Gwamna Zai Kawo Wa APC Nasara A Katsina”
“Ganawar ta yi mana dadi kuma za a ci gaba da gudanar da makamanciyarta tsakanin bangarorin biyu”, in ji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, wadanda suka halarci taron daga bangaren Tinubu sun hada da Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, da na Jihar Ekiti Kayode Fayemi.
Daga bangaren Wike kuma akwai Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, da na Jihar Oyo Seyi Makinde.
Rahotanni dai na nuna cewa ana kokarin cimma matsaya ne kan ko Wike zai dawo APC, ko kuma zai yiwa Tinubu aiki daga jam’iyyarsa ta PDP a zaben shugaban kasa na 2023.
Wani tsohon minista da ke tsagin Wike, ya ce bai ga abin tada jijiyar wuya don Wike da Tinubu sun yi taron ba, domin shi ma dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar na yin makamancinsa da gwamnonin APC.
Yunkurin ji ta bakin Festus Keyamo, kakakin tawagar yakin neman zaben dan takarar APC, da kuma daraktan yada labarai Bayo Onanuga, da kakakin Tinubu, Tunde Rahman, ya ci tura, domin ba su amsa kira da sakonnin da aka tura musu ba.
A hannu guda kuma kakakin Atiku, Paul Ibe ya ki cewa komai kan lamarin.
Tun a baya dai tsohon ministan ayyuka, kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Adeseye Ogunlewe, ya shawarci Wike da ya koma wajen Tinubu bisa zargin watsi da shi a siyasance da PDP ta yi.
Sai dai a wata hira da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi da gidan talabijin na Channels, ya ce babu wanda ya bata wa Wike rai, kuma bai ga abin da aka masa ba.