A yayin da jam’iyyun siyasa suka fara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027 duk da akwai kusan shekaru biyu; masana da masu ruwa da tsaki sun bukaci a kawo karshen matsalar sayen kuri’a da ke kawo cikas ga mulkin dimokuradiyya.
Gurbatattun ‘yan siyasa na cin karen su ba babbaka ta hanyar amfani da kudi da kayan masarufi wajen sayen kuri’u wanda hakan babban laifi ne da ya sabawa kundin dokar zabe ta 2010.
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe.
- Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam
A zaben 2023 an gudanar da shari’un zabe 1, 196 wanda daga ciki akwai dimbin korafe- korafe kan sayen kuri’ar masu zabe da jami’an zabe wanda ya zama dalilin bayyana wadanda ba su samu nasara ba a matsayin wadanda suka yi galaba wanda hakan babban kalubale ne ga mulkin dimokuradiyya.
Masu fashin bakin lamurran siyasa sun bayyana cewar zaben 2027 zai yi matukar zafin da zai dama ya shanye na 2023 nesa ba kusa ba musamman yadda tun a kasa da shekaru biyu jam’iyyun adawa suka daura damarar kawar da gwamnati mai ci kamar kuma yadda su kan su al’umma da dama suka kagara lokacin zaben ya yi a bisa ga halin matsin da suke ciki.
Sayen kuri’a da mabambantan ‘yan takara da jam’iyyun su ke yi na kan gaba wajen kawo tangarda da cikas ga mulkin dimokuradiyya ta hanyar murde zabe da ke zama silar samun nasarar wadanda ba su cancanta da mulkin jama’a ba.
A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu.
A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben.
Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ke yi, galibi ba a cika jin sun gurfanar da masu aikata wannan danyen laifin a gaban kotu ba wanda hakan ya yi tasiri wajen ba su damar ci-gaba da cin karen su ba babbaka.
A bisa ga amfani da kudi wajen sayen kuri’u jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su na samun nasarar kayar da nagartattun ‘yan siyasar da ke da ingantattun kudurori da manufofin inganta rayuwar al’umma.
Hukumomin yaki da cin na EFCC da ICPC a kowane zabe kan bayyanawa al’umma illar sayen kuri’a tare da kira ga al’umma da su kwarmata bayanin sayen kuri’a tare da tukaicin samun na goro ga duk wanda ya bayar da rahoton amfani da kudi wajen sayen kuri’a, sai dai duk da hakan matsalar ta’azzara take yi ba raguwa ba.
Hukumar kididdiga ta Nijeriya wato NBS ta tabbatar da cewar an samu yawaitar sayen kuri’a da sayar da ita a babban zaben 2023 da ya gabata a dukkanin zabuka.
A rahoton da hukumar ta fitar kan cin hanci a Nijeriya ta bayyana cewar a zaben 2023 an samu yawaitar sayen kuri’a kashi 22% wanda ya karu sama da kashi 5 a kan na zaben 2019 da kashi 17%.
A cewar NBC a rahoton da ta fitar a Yuli 2023 ‘yan Nijeriya kashi 22% ne suka kai rahoton an ba su kudi domin sayen kuri’un su kafin da yayin zaben 2023, a yayin da kashi 9 aka ba su wasu abubuwan daban
“A 2023 kashi 10 na mutane sun bayyana cewar ba a ba su kudi domin sayen kuri’a ba amma an baiwa wani daga cikin ‘yan gidan su wanda ya wuce na 2019 da kashi 5.
Sai dai hukumar ta bayyana cewar kashi 55 na ‘yan Nijeriya da aka baiwa kudi ko kayan masarufi domin sayar da kuri’a sun bayyana cewar cin hancin bai canza ra’ayin su ba, to amma kashi 40 sun bayyana cewar sun zabi jam’iyya ko dan takarar da ya ba su kudi.
A kan gagarumar matsalar sayar da kuri’a da illar ta ga zabe mai zuwa, tuni masana da masu ruwa da tsaki suka fara kira ga al’umma da su tashi tsaye su yaki matsalar wadda ke hanawa mulkin dimokuradiyya ci-gaba mai ma’ana.
Tsohon Gwamnan jihar Bayelsa kuma Sanatan da ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, Sanata Henry Seriake Dickson na kan gaba wajen bukatar al’umma da hukumomin da lamarin ya shafa da su daura damarar kawar da matsalar sayen kuri’a da buga sakamakon zaben bogi.
Sanata Dickson ya bayyana hakan ne a bayanin da matainakinsa kan yada labarai a Arewa, Jamilu Abubakar ya fitar yana cewar masu ruwa da tsaki da ‘yan Nijeriya bakidaya suna da hakkin gyara abubuwan maras kyau da ke faruwa a kasar nan.
Tsohon Gwamnan ya ce gurbatattun abubuwan da ke gudana a karkashin jagorancin masu hali da ‘yan siyasa masu fada aji lamari ne da zai tarwatsa tsarin siyasar kasar nan.
Sanatan ya bayyana fatara da rashin sani a matsayin kashin bayan da gurbatattun ‘yan siyasa ke amfani wajen samun kuri’a ta hanyar amfani da kudi da kayan masarufi.
Ya ce wannan matsalar ta jefa ‘yan Nijeriya a cikin kunci da mayar da kasa baya domin mutanen da ba su cancanta ba ke rike da mukamai wadanda babu nauyin da suke saukewa bayan samun nasara.
“Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomi.”
“Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori kara mai kyau ta fashin zabe.” Ya bayyana.
Ya ce irin wannan matsalar na samar da mutanen da ba su ko iya cin zabe a cikin dangin su ko al’ummar su amma sune ke tinkahon lashe zabe.
A cewarsa a matsayinsa na dan majalisar dattawa suna kokarin gabatar da dokokin da za su shawo kan wadannan matsalolin, ya ce sun san hukumar zabe ba za ta iya kula da abubuwan da jami’an tsaro ke yi a yayin zabe ba.
“Shi ne dalilin da yasa ake canza sheka zuwa jam’iyya mai mulki domin samun damar amfani da madafun ikon cin zabe ta kowace irin hanya.”
A wani bincike da Cibiyar Ayyukan Majalisa da Dimokuradiyya a Nijeriya ta gudanar ta bayyana cewar sayen kuri’a ya samu gindin zama a farfajiyar siyasar Nijeriya wanda ya kamata a dauki kwakkwaran matakin shawo kan matsalar.
Cibiyar ta bayyana cewar hakan ya faru ne saboda jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su sun nuna a fili a yayin yekuwar neman zabe cewar jam’iyyun da ke da ingantattun manufofi da nagartattun ‘yan takara ba su isa su kadai su tabbatar da nasarar zabe ba wanda shine dalilin da yasa suka zabi sayen kuri’a.
Haka ma su kan su masu zabe sun nuna amincewar a ba su kudi su sayar da ‘yancin su ga wanda zai bada kudi mafi yawa a kowane irin zabe wanda hakan babban kuskure ne da ke haifar da zaben tumun dare.
A binciken da cibiyar ta gudanar ta bayyana cewar sayen kuri’a na yin tasiri kwarai wajen canza ra’ayin masu zabe wanda babban kalubale ne ga dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a Nijeriya musamman hukumar zabe.
Idan har za a gudanar da zaben gaskiya da adalci ya kuma zama mai amfani ga ingantaccen mulki to wajibi ne a yaki matsalar sayen kuri’a kamar yadda cibiyar ta jaddada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp