A wani bangare na kokarin gina hadakar jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027, jam’iyyar ta fara tusashe karfin PDP a wasu jihohin Nijeriya sakamakon jan hankalin manyan ‘yan siyasa daga PDP da APC.
Duk da cewa ADC ta riga ta karbe tsarin PDP a Yobe, Gombe, Adamawa da wasu jihohi na arewa, amma mafi yawancin masana harkokin siyasa suna ganin cewa akwai sauran rina a kaba.
- Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista
- EFCC Ta Kama Ƴan Ƙasashen Waje 146 Kan Laifukan Zambar Kuɗaɗe
Wannan ya zo ne tun bayan da Gwamna Jihar Borno, Babagana Zulum ya musanta rahotannin kafafen watsa labarai cewa zai jagoranci wasu gwamnonin guda biyar daga APC zuwa ADC.
Haka kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyar LP a 2023, Mista Peter Obi, ya ce zai ci gaba da kare muradun magoya bayansa da abokan siyasarsa.
Sannan ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki sakatare na wucin gadi na ADC, Rauf Aregbesola, kan ya bayar da rahoton aikinsa a matsayinsa na ministan harkokin cikin gida a lokacin mulkin da ya gabata.
Da yake tabbatar da daukar salon tsarin PDP a jihohin Yobe, Gombe da Adamawa, Mista Paul Ibe, mai ba da shawara kan harkokin watsa labarai ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce shugabannin PDP a jihohin arewa sun yi hadin gwiwa da hadakar jam’iyyar.
Ibe ya ce: “Hadakar na samun karfi. Atiku Abubakar zai ci gaba da bayar da gudunmuwa don tabbatar da cewa hadin gwiwar na jam’iyyar.”
“Bayan samun hakan, za ka iya ganin sakamakon. Shugabannin PDP na Yobe sun hade da ADC, haka ma na Gombe. Shugabannin Adamawa ma sun yi alkawarin amincewa. Wannan lamari yana samar da sakamakon da ake bukata.”
Haka kuma ya da yabawa rawar da Atiku ya taka wajen hada kan kungiyoyi daban-daban na siyasa, yana bayyana hakan a matsayin alamar shugabanci na gari.
“A makon da ya wuce, tsarin siyasa yana juyawa zuwa ga mulkin jam’iyya guda, wanda ya tuna da zamanin Abacha. Wannan hadakar tana mayar da martani ne ga irin wannan barazana,” Ibe ya shaida hakan.
Ya kwatanta kalubalen gina hadakan da cewa kamar sabbin ma’aurata ne da ke daidaita rayuwa tare
Shugaban kungiyar shugabannin PDP na jihohi (PDPSCF), da kuma shugaban PDP na Jihar Imo, Mista Austin Nwachukwu, ya bayyana rahotannin tusashewar a matsayin shadi fadi, yana mai jaddada cewa PDP na nan da karfi da hadin kai.
Nwachukwu ya ce, “Shugabannin jam’iyyar a Yobe da Borno sun ki yarda da wannan ikirarin. Wadannan labaru ne na boge da aka kirkira don jawo hankalin al’umma.
“Yawancin wadannan ‘yan siyasarmu sun haura shekaru fiye da 70. Me suke nema a yanzu? Kudaden ritaya ko yi wa kasa hidima.”
A cewarsa, PDP ta kasance kan duga-duganta, yayin da ya yi watsar da labarin dusashewar a matsayin abin da ba shi da tasiri. Ya ce, “Da yawa daga cikin wadanda suka fita sun koma PDP. Muna waADC fatan alkairi, amma PDP ta fi karfin ta dusashe ta a kowanne lokaci.”
A halin yanzu, mai magana da yawun ADC na wucin gadi, Bolaji Abdullahi, ya jaddada cewa hadakar na da tasiri dun tunkarar APC mai mulki a 2027.
A cikin wata tattaunawa da manema labarai, Abdullahi ya ce, “ADC na wakiltar hadakar ‘yan Nijeriya da ke tsayawa kan gazawar wannan gwamnati. A cikin watannin da ke tafe, za ku ga ba mambobin PDP ba kadai har ma da wasu jam’iyyun adawa kamar SDP, LP, da NNPP za su shigo cikinmu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp