Lauyoyin Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, wato Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sun miƙa takardun hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a satin da ya gabata na cewa majalisar dattawa ta gaggauta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Natasha kuma a bata dama ta koma bakin aiki a zauren majalisa.
A wata wasiƙa da lauyoyin Sanata Natasha suka rubuta zuwa majalisar, sun bayyana cewa Sanatar za ta koma aikinta na wakiltar mutanenta a ranar Talata, 15 ga watan Yuli, kamar yadda kotu ta yanke hukunci.
- Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
- Lauyoyin Majalisar Dattawa Sun Ƙaryata Natasha Kan Cewa Kotu Ta Ce Ta Koma Bakin Aiki
Hukuncin da kotun tarayya ta yanke a ranar 4 ga watan Yuli ya nuna cewa dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya yi yawa kuma ya saɓawa doka sannan kuma an tauye mata haƙƙinta na wakiltar mutanenta a majalisar dattawa ta ƙasa. Kotun ta kuma ce matakin da aka ɗauka a kan Natasha ya saɓawa sashi na 63 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan, sannan ya kuma saɓawa dokar majalisa wadda ta bayar da dama a dakatar da wakili iya kwanaki 14 kacal.
Lauyoyin Sanata Natasha sun ce hukuncin kotun ya yi daidai da shashi na 318 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, sannan sun yi kira ga majalisar da ta bi umarnin kotu ta gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa Sanatar.
Lauyoyin Sanatar sun ce tun da majalisa tana da ikon dakatar da wakili, hakan yana nufin tana da ikon dawo da wadda aka dakatar domin a bata dama ta ci gaba da wakiltar mutanenta da suka je suka zaɓe ta a ranar zaɓe domin ta wakilce su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp