Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana wasu muhimman wurare da take ganin ya kamata a maysr da hankali a kansu wajen sake duba Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana buƙatun a cikin bukatun da Kano ke so a saka a cikin sabon tsarin mulki, daga ciki akwai a bai wa jihohi ƙarin ikon mallakar albarkatun ƙasa da kuma ƙarin kaso daga asusun tarayya.
- Kawu Sumaila Ya Yabi Gwamnatin Kano Kan Goyon Bayan Kirkiro Sabuwar Jihar Tiga
- Manyan Batutuwan Taron Sanatoci Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya A Kano
Haka kuma gwamnatin Jihar na so a bai wa jihohi damar samar da jami’an ’yansanda na jiha da kula da harkokin tsaro kai tsaye domin inganta zaman lafiya.
Gwamnan wanda mataimakinsa, AminubAbdussalam Gwarzo ya wakilta ya ce; Gwamnatin ta Kano na buƙatar a samar da ’yancin ƙananan hukumomi tare da da yin adalci wajen rabon kuɗaɗen su, sannan a samar da tsarin shugabanci nagari wanda zai haramta duk wani yunkuri na mulkin kama-karya.
Sauran buƙatun da jihar Kano ta miƙa sun haɗa da sake duba tsarin rabon kujeru a majalisar dattawa da ta wakilai, ƙarfafa ikon majalisun jihohi kan gwamnoni da kuma tsara zaɓe me nagarta.
Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa gyaran kundin tsarin mulki zai taimaka wajen kare haƙƙin ’yan ƙasa da tabbatar da adalci a tsakanin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp