Tsohon shugaban ƙasa, Janaral Ibrahim Badamasi Babagana ya bayyana alhininsa bisa rasuwar abokinsa kuma tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi 13, ga Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan.
Babangida ya ce: “Ina cike da alhini da juyayi na samun labarin rasuwar abokina, ɗan’uwana, abokin karatuna a makarantar soja, kuma abokin gwagwarmayar gina ƙasa, Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, GCFR.”
- Sarkin Musulmi, Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
- Na Yi Rashin Nagartaccen Abokin Aiki, Mai Dattako, Shugaba Buhari —Jonathan
“Mun fara haduwa da shi a shekarar 1962 lokacin da muka shiga Kwalejin Horan Sojoji ta Nijeriya da ke Kaduna. Tun daga wancan lokaci, Muhammadu Buhari ya fara bambanta kansa da saura, saboda mutum ne mai ƙarfin zuciya da tsarin rayuwa, kuma ɗan kishin ƙasa mai ƙaunar ci gaban Nijeriya. Mun sha wahala tare, mun kuma yi faɗi-tashi tare. Ƙaunar ƙasa da ƙwarewa a aiki su ne suka haɗa mu wuri guda, ba kawai aikin soji ba.” In ji Babangida
Janar Babagida ya ci gaba da cewa: “A cikin aikinmu, ƙaddara ta sa kowannenmu ya shugabanci Nijeriya a lokuta daban-daban da yanayi daban. Amma a kowane lokaci, Buhari ya kasance mai kishin gaskiya da bin tsarin mulki da martabar shugabanci. Ya yi wa Nijeriya hidima da amana da jajircewa ko da kuwa a wasu lokutan wasu ba su fahimce inda ya dosa ba.”
“Bayan aikin soji, na san shi a matsayin mutum mai tsoron Allah, wanda yake da nutsuwa da riƙo da addininsa, kuma yana rayuwa da tawali’u da rayuwa akan manufa. Duk da cewa ba koyaushe ra’ayinmu yake zuwa ɗaya ba, kamar yadda yake a tsakanin ‘yan uwa, amma ban taɓa shakkar gaskiyarsa ko kishin ƙasarsa ba,”
“Rasuwar Buhari ba kawai rasa tsohon shugaban ƙasa ba ne, ko shugaban da aka zaɓa sau biyu a mulkin dimokuraɗiyya ba. Rasa shi babban rashin mutum ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen haɗa tsohuwar Nijeriya da sabuwar jamhuriya. Ko a lokacin da ya yi ritaya, ya kasance abin koyi da nagarta da gaskiya ga mutane da dama.”
A ƙarshe tsohon shugaban ƙasar, ya yi addu’a ga marigayi Buhari tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga matarsa Aisha da ‘ya’yansa, da jikokinsa da dukkan jama’ar Nijeriya da ya yi wa hidima. “Allah ya gafarta masa, ya karɓi ayyukansa na alheri, ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus.” In ji Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban Nijeriya, a cikin wani sakon ta’aziyya da ya aike a ranar Lahadi 13, Yuli 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp