Gawar tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yanzu haka tana kan hanyar zuwa garinsa na haihuwa, Daura, domin gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ana isar da gawar marigayin ta hanyar mota daga Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan karramawa ta musamman da dakarun Sojoji suka gudanar.
Gawar Buhari ta iso Nijeriya daga Landan inda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, yana da shekaru 82. Manyan jami’an gwamnati da danginsa sun hallara domin kasance wa ta ƙarshe tare da shi.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya da ta dawo da gawar daga Ingila, bisa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Tinubu da kansa ya isa Katsina da wuri domin karɓar gawar tsohon shugaban ƙasar, tare da Gwamna Dikko Umar Radda da sauran manyan jami’an gwamnati.
An shirya gudanar da jana’izar marigayin a ranar Talata da rana a Daura, inda ake sa ran dubban mutane daga ciki da wajen Nijeriya za su halarta, ciki har da shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, da wakilan ƙasashen waje, domin girmama mutumin da aka fi saninsa da suna “Mai Gaskiya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp