Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da bayyana dalilan sa da suka shafi saɓani da karkacewar jam’iyyar daga ainihin manufofinta na kafuwa.
A wata wasiƙar da aka sanya wa kwanan wata 14 ga Yuli, 2025, wacce ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Jada 1, a ƙaramar hukumar Jada ta jihar Adamawa, Atiku ya rubuta cewa: “Ina rubuto wannan wasiƙar ne don sanar da ku hukuncin ficewata daga jam’iyyar PDP daga wannan rana.”
- Ina Cike Da Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari — Atiku
- Zan Yaƙi Duk Wanda Ya Yi Sata Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Atiku
Atiku, wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 tare da kasancewa ɗan takarar shugaban ƙasa sau biyu a ƙarƙashin PDP, ya bayyana cewa wannan mataki yana da matuƙar nauyi da raɗaɗi a zuciyarsa. “A matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa wannan jam’iyya mai daraja, ficewa daga cikinta abu ne mai matuƙar raɗaɗi gare ni.”
Ya ƙara da cewa akwai saɓani da aka gaza sulhu tsakaninsa da jam’iyyar, inda ya bayyana cewa PDP ta gushe daga ainihin hanyarta. “Na yanke shawarar ficewa ne saboda yadda jam’iyyar ke tafiya yanzu ya sha bamban da manufofin da muka tsaya a kai tun farko.”
Atiku ya kammala wasikar da godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da goyon bayan da ya samu tsawon shekarun da ya kwashe a cikinta. “Ina fatan jam’iyya da shugabanninta za su yi nasara a gaba. Na gode bisa damar da aka ba ni.”
An tabbatar da karɓar wasiƙar ficewar a ofishin gundumar PDP ranar 14 ga Yuli, 2025, tare da sanya hannu da hatimin karɓa daga wani wakili mai suna Hamman Jada Abubakar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp