‘Yan kasuwan man fetur a Nijeriya sun sanar da rage farashin man fetur wanda ya fara aiki daga ranar Talata.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamantin tarayya ta bayar da hutu na musamman domin alhinin rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
- Afrika Ta Zama Kasuwar Sayar Da Man Fetur Mara Inganci – Dangote
- Akwai Bukatar Daina Cin Zarafin Malaman Makaranta
Shugaban kungiyar Dillalan Man fetur a Nijeriya (IPMAN), Abubakar Maigandi, shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a hirarsa da ‘yan jarida.
A cewarsa, daukan matakin rage farashin ya biyo bayan zaman ganawa da mambobin IPMAN suka yi a Abuja ne ranar Litinin dangane da sauke farashin litar man fetur da matatar mai ta Dangote ta yi kwanakin baya zuwa naira 820 daga naira 840 kan lita guda.
A fadinsa, mambobin IPMAN daga ranar Talata za suke sayar da litar mai daga yankin Abuja a kan tsakanin naira 900 zuwa naira 920 a kan kowace lita, sabanin yadda suke sayarwa daga naira 905 zuwa 945 a baya.
“Kazalika, mambobinmu a wasu sassan kasar nan za su sayar da litar mai tsakanin naira 860 zuww naira 890 kan kowace lita.
“Yan Nijeriya na murna saboda ana ta samun raguwar farashin mai a makwanni biyu da suka wuce,” ya shaida.
Matakin na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwana guda domin nuna alhini da juyayin rayuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda aka birne shi a garin Daura da ke Jihar Katsina bayan da ya rasu a ranar Lahadi 14 ga watan Yulin 2025 a kasar Ingila, yayin da ya je jinya. IPMAN dai ta fara rage farashin mai ne a makon da ya wuce.
Idan za a tuna dai matatar man Dangote ta rage farashin litar man a makon da ya wuce daga naira 840 zuwa 920.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp