Tsohon ɗan majalisar tarayya da ya wakilci Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa ta 8, Barrista Dino Melaye, ya fara bayyana a kotu a matsayin lauya a ranar Juma’a, inda ya bayyana cikin cikakkun shigar kayan lauyoyi a Babban Kotun Tarayya ta 8 da ke Abuja.
Ya bayyana a gaban kotun Mai Shari’a Emeka Nwite na Kotu ta 8, kamar yadda ya bayya a shafinsa na Facebook.
- ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
- An Kama Mutane 26 Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Kogi
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa Melaye, jigo a jam’iyyar ADC, na daga cikin sabbin lauyoyi sama da 5,000 da aka yaye a Abuja a farkon watan Yuli, bayan ya kammala karatunsa na digiri a fannin lauya a jami’ar Baze.
Bayyanarsa a ranar Juma’a ta nuna fara aikinsa a bainar jama’a a matsayin lauya, wanda abokansa suka bayyana a lamarin a matsayin wani sabon babi a rayuwarsa ta gwagwarmaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp