Gwamnatin tarayya ta bayyana yiwuwar samun kudaden shiga da yawansu ya kai kimanin Naira tiriliyan uku, a aikin tatsar man Rogo a Nijeriya duk shekara.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya sanar da haka, a taron bikin ranar Rogo ta duniya na 2025, wanda aka gudanar a dakin taro na Bankuet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.
- Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa
- Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi
Ya sanar da cewa, tuni gwamnatin tarayya ta fara ayyukan kirkirar fasahar zamani, domin zamanantar da masana’antar sarrafa Rogo a wannan kasa.
“Daya daga cikin kirkirar fasahar ita ce, ta aikin tatsar man Rogo, wanda kuma ake sa ran aikin zai iya samar wa da Nijeriya kimanin Naira tiriliyan uku a duk shekara, wanda kuma hakan zai sanya kasar rage dogaro da shigo da man fetur daka kasashen waje,” in ji Kashim.
“Karin babban muhimmancin shi ne, aikin zai kuma taimaka wajen masana’antun kasar; wajen samun saukin sarrafa man da ake samu daga Rogon,“ a cewar mataimakin.
“Dole ne mu yi amfani da sauran kayan da ke cikin Rogo, tun daga bawonsa, wanda hakan zai sanya Nijeriya kai wa ga wani mataki na gaba wajen fitar da shi zuwa kasuwannin duniya,” in ji shi.
Kazalika, Shettima ya kaddamar da aikin kimiyyar, wanda aka samar da shi don rubunyya Irin Rogon da ake shukawa.
A cewarsa, aikin zai kuma rage gibin da ake da shi na yin noman Rogo, domin samun riba tare kuma da samar da ingantaccen Iri.
Ya sanar da cewa, kasar nan, na yin koyi ne kan nasarorin da kasar Ethiopiya ta samu, kan wasu amfanin gona yadda manoma, musamman kanana za su yi noma tare da samun riba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp