Gwamnatin Jihar Nasarawa, karkashin hadakar da ta kulla da gwamnatin tarayya, ta fara rabar da takin zamani 74,800, a daukacin fadin jihar.
Har ila yau, ta yi hakan ne domin kara bunkasa yin girbin amfanin gona a jihar.
Kowane manomi daya, zai samu Buhu daya, inda aka ware Buhununa guda 500, domin a raba wa manoman da aka zabo daga mazabu 147, sai kuma Buhuhuna guda 100 za a rabar a kananan hukumomi 13 na jihar.
A jawabinsa a wajen taron rabar da takin a garin Lafia, gwamnan jihar Abdullahi Sule ya bayyana cewa; yana da yakinin cewa; manoman da suka amfana da takin za su yi amfani da shi, domin kara habaka aikin noma a fadin jihar.
Ya kuma gode wa Shugaban Kasa Bola Tinubu, kan hanyar da ya yi na samun takin, inda ya bayyana cewa; hakan zai kara samar da wadataccen abinci a jihar da kasa baki-daya da kuma kara habaka fannin a jihar.
Duk a cikin kokarin da gwamnatinsa ke yi na habaka fannin, gwamnan ya bayyana cewa; ta sanya a noma hektar noma guda 2000 ta Shinkafa a yankin Jangwa na Karamar Hukumar Awe tare kuma da karin noma wasu hektar noman guda 3,500 a yankin Danka/Ayarkeke da ke Karamar Hukumar Obi, a cikin wannan shekarar.
Gwamna Sule, ya kuma gargadi wadanda aka dora wa nauyin rabar da takin, kan karkatar da takin; wanda ya sanar da cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunta ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp