Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sauya sunan sabon titin Shendam da aka kammala kwanan nan, ya sanya masa sunan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Titin mai layi biyu an buɗe shi ne ta hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin ziyararsa ta kwana ɗaya a jihar a ƙarshen watan da ya gabata.
- Matsalolin Rayuwa: Matasan Suleja Na Buƙatar Ƙarfafa Gwuiwa
- Za A Dinga Tunawa Da Buhari A Matsayin Waliyyi A Siyasar Nijeriya —Dakta Zangina
A yayin wani taron addu’a na musamman da aka gudanar a Lafia domin girmama marigayi Buhari, Gwamna Sule ya bayyana cewa sanya sunansa a kan wannan titi wata hanya ce ta tabbatar da girmamawa da ɗaukaka ga tsohon shugaban ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa za su aika da ƙudirin doka zuwa majalisa domin samun cikakken goyon bayan doka wajen sauya sunan titin daga Shendam Road zuwa Muhammadu Buhari Way.
A nasa jawabin, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yabawa wannan yunƙuri na Gwamna Sule da kuma rawar da Sarkin Lafia ya taka wajen shirya addu’o’in karrama marigayi Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp