Ƙoƙarin hana Sanata Natasha Akpoti-Uduagha daga ci gaba da aiki a Majalisar Dattawa barazana ce ga cigaban dimokuraɗiyya a Nijeriya, in ji Kwamared Steve Aluko, wanda shi ne ko’odinetan ƙungiyar kare ‘yancin ɗan adam ta yankin Arewa ta Tsakiya (CLO).
Sanata Natasha ta rubuta wa Sufeto Janar na ƴansanda, inda ta sanar da niyyarta ta komawa bakin aiki, tare da roƙon a maido da jami’an tsaron da aka sa mata. Amma sai gashi a ranar Talata, jami’an tsaro sun hana ta shiga Majalisar Tarayya duk da wata hukuncin kotu da ta ba ta damar komawa kujerarta.
- Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro
- ‘Ka Da Ki Kuskura Ki Zo Majalisar Tarayya’, Majalisar Dattawa Ta Sake Yi Wa Natasha Gargaɗi
Aluko ya bayyana hakan a wata hira da LEADERSHIP a Jos, babban birnin jihar Filato, inda ya ce wannan mataki yana ƙara bayyana gazawar Majalisar Dattawa ta 10 wajen kare tsarin mulki da doka. Ya ce abin da ke faruwa ba ya wakiltar muradun ƙasa, sai dai na wasu mutane da ke da wata manufa ta siyasa.
Ya zargi ofishin Sufeto Janar na ƴansanda da ƙin yin aiki da korafe-korafen da aka aika musu dangane da batun, inda ya ce hukumar ƴansanda ta gaza kare Sanata Natasha da tabbatar da ta koma bakin aiki lafiya bisa doka. A cewarsa, hana ta shiga majalisar “ba bisa ka’ida ba ne, kuma ya ci karo da hukuncin kotu da ya tabbatar da dawowarta.”
Aluko ya jaddada cewa, muddin babu wani sabon hukuncin kotu da ke soke wanda aka riga aka bayar, to babu wata hukuma ko mutum da zai hana ta komawa aiki. Ya ce wannan lamari ya nuna rashin mutunta kundin tsarin mulki, kuma zalunci ne ga mazabar da Sanata Natasha ke wakilta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp