• English
  • Business News
Sunday, September 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai

by Sulaiman
2 months ago
in Labarai
0
Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da cikakken goyon baya ga ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin ’yan jarida, tare da fahimtar muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen gina ƙasa.

 

Da yake jawabi a taron lacca na shekara-shekara na kamfanin jaridar Blueprint wanda aka gudanar a ranar Talata a Abuja, Idris ya ce tun farkon naɗin sa, Shugaba Tinubu ya bayyana masa cewa ya ba shi dama ya yi aikin sa yadda ya ga ya dace a matsayin sa na ƙwararre.

  • Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi,  Jafaru Ilelah, Rasuwa
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babban mai goyon bayan kafafen yaɗa labarai ne. Yana da masaniyar cewa kafafen yaɗa labarai suna da matuƙar muhimmanci wajen gina ƙasa, kuma ya sha gaya mini cewa in ci gaba da aiki na yadda na ga ya dace, kasancewa ta ƙwararre.”

 

Labarai Masu Nasaba

Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin Naira

Wannan Bishiya Ta Bayyana Sirrin Ci Gaban Jihar Xinjiang

Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa al’umma tana ci gaba da zama cikin haɗin kai, yayin da muke riƙe shugabanni da gwamnati da alhakin aikin su.”

 

Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen kula da tsarin dimokiraɗiyya, inda ya shawarci ’yan jarida da su kula da rawar da suke takawa domin kada su zama abin da zai jawo ruɗani ko rikici a cikin al’umma.

 

“A yayin da kuke yin wannan aiki, kuna da babban nauyi na riƙe gwamnati da shugabanni da alhakin aikin su. Amma ko da kuna yin hakan, dole ne ku sani cewa saboda matsayin ku na musamman da rawar da kuke takawa, za ku iya taimaka wa ƙasa matuƙa, amma idan ba a yi taka-tsantsan ba, ayyukan ku na iya cutar da al’umma,” inji shi.

 

Ya bayyana buƙatar sanin ya kamata da hankali wajen tantance sahihin bayani daga wanda zai iya ɓata zaman lafiya ko raba kan al’umma.

 

Ministan ya ce duk da ƙalubalen da ke fuskantar fannin yaɗa labarai, akwai haske a gaba domin kafafen sun ci gaba da nuna jajircewa da ɗorewa.

 

Ya kuma bayyana cewa ba shi ba ne Shugaban kamfanin jaridar Blueprint ba tun bayan da aka naɗa shi Minista.

 

“Ba ni ne shugaban jaridar Blueprint ba yanzu. Ni ma baƙo ne aka gayyata zuwa wannan taro. Na san cewa a baya ni ne ke gaba wajen shirya wannan taron na Blueprint, musamman tun lokacin da aka kafa ta shekaru 14 da suka wuce. Dole ne in gode wa waɗanda aka gayyata su haɗu da ni a watan Mayun 2005 domin tunanin fara jaridar Blueprint: Malam Ibrahim Sheme; Manajan Darakta, Malam Salisu Umar; Shugabar Kwamitin Tace Labarai, Hajiya Zainab Okino, da dukkan ma’aikatan jaridar Blueprint.

 

“Na gode da cigaba da tafiyar da abin da muka faro cikin nasara. Na shekara guda ban ziyarci ofishin ba, amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi hakan. Ina so in ga ko har yanzu kuna ci gaba da tafiyar da abin da muka faro. Ina alfahari kuma ina farin ciki da cewa abin da muka fara ya ci gaba da bunƙasa,” inji shi.

 

Idris ya taya waɗanda suka samu kyaututtuka murna, inda ya bayyana cewa ba a yi masu kyautar bisa wani son zuciya ko tasiri daga wani waje ba, sai hukuncin jaridar ne kaɗai.

 

Cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake; Ministan Raya Noman Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha; Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, da babban baƙon jawabi na taron, Farfesa Attahiru Jega.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — Tinubu

Next Post

Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati

Related

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin Naira

5 hours ago
Wannan Bishiya Ta Bayyana Sirrin Ci Gaban Jihar Xinjiang
Ra'ayi Riga

Wannan Bishiya Ta Bayyana Sirrin Ci Gaban Jihar Xinjiang

10 hours ago
Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu
Rahotonni

Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu

12 hours ago
Ana Hasashen Tashin Fetur Idan Matatar Dangote Ta Daina Karɓar Naira
Manyan Labarai

Ana Hasashen Tashin Fetur Idan Matatar Dangote Ta Daina Karɓar Naira

12 hours ago
Rashin Aikin Yi: A Halin Yanzu Masu Digiri Na Sayar Da Fiya Wata Da Aikin Achaba
Rahotonni

Rashin Aikin Yi: A Halin Yanzu Masu Digiri Na Sayar Da Fiya Wata Da Aikin Achaba

15 hours ago
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna
Labarai

Uba Sani Ya Jagoranci Yunƙurin Ƙara Yawan Rajistar Masu Zaɓe a Jihar Kaduna

15 hours ago
Next Post
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma'a - Gwamnati

LABARAI MASU NASABA

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin Naira

September 27, 2025
Shugaban Cuba Ya Yi Bayani Kan Nazarin Fasahohin Sin A Fannoni Shida

Shugaban Cuba Ya Yi Bayani Kan Nazarin Fasahohin Sin A Fannoni Shida

September 27, 2025
Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu

Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu

September 27, 2025
Me Ya Sa Kamfanonin Jamus Fiye Da 560 Suka Zabi Wani Gari A Kasar Sin Don Gudanar Da Harkokinsu?

Me Ya Sa Kamfanonin Jamus Fiye Da 560 Suka Zabi Wani Gari A Kasar Sin Don Gudanar Da Harkokinsu?

September 27, 2025
Matsalar Tasgadewar Kashin Baya

Matsalar Tasgadewar Kashin Baya

September 27, 2025
Firaministan Sin: Adalci Shi Ne Abu Mafi Daraja A Wurin Kasashen Duniya 

Firaministan Sin: Adalci Shi Ne Abu Mafi Daraja A Wurin Kasashen Duniya 

September 27, 2025
Yadda Ake Hada Sushi

Yadda Ake Hada Sushi

September 27, 2025
Ribar Da Manyan Kamfanonin Kasar Sin Ke Samu Ta Dawo Turbar Karuwa A Watanni 8 Na Farkon Bana

Ribar Da Manyan Kamfanonin Kasar Sin Ke Samu Ta Dawo Turbar Karuwa A Watanni 8 Na Farkon Bana

September 27, 2025
Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano

Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano

September 27, 2025
Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang

Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang

September 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.