Jihar Filato ta kasance daya daga cikin jihohin da ke a kan gaba wajen masana’antun da ke samar da kwan gidan gona.
Ta kuma kasance a kan gaba wajen samar da sana’oin yi, musamman ganin ana da sama da gidajen da ake yin kiwon Kajin gidan gona 4,000, inda kusan masana’antun da ake yin kiwon Kajin, kida da ma;aikata da suka kai daga 10 zuwa 20.
Sai dai, wasu kalubale sun yiwa masana’antun daurin demon minti, inda hakan ya tilasta wasu daga cikin masana’antun dakatar da yin aiki ko kuma daina yin sana’ar baki daya.
Wadanda kuma suka jure ci gaba da yin sana’ar, suna samar da kwan kasa da yadda suke samar wa a baya.
Wasu daga cikin manyan matsalolin sun hada da tsadar abincin su, da magungunna su da rashin samun kasuwa.
Bugu da kari, kafin wannan akwai kuma bullar cutar murar tsintsaye wacce ta janyo raguwar kajin na gidan gona, haka hunturun da aka yi a shekarar da ta wuce ya shafi fannin saboda sanyin da aka yi mai tsanani, inda sanyin ke janyo raguwar kwayayen da ya kamata a kyankyashe.
Kari akan wannan kalubalen da kunno kai a yanzu a jihar shine, shirin sauya sabbin kudi dababban bankin Nijeriya ya fito da shi.
Wannan kalubalen ya janyo shugaban kungiyar masu kiwon Kajin reshen jihar Johnson Bagudu ankarar da bankin akan illlar da hakan ya haifar wa da fannin nasu, iinda ya ce, lamarin na ci gaba da kara munana.
Bagudu ya ce, kalubalen ya janyo karyewar farashin kwan wanda a baya ake sayar da kirat kan Naira 2,100 amma a yanzu, ana sayar da shi kan Naira 1,000, inda ya ce wannan ya haifarwa da masu yin asara.
Ya ce, hakan ya janyo kwan ya yi kwantai saboda wasu masu kiwon sun gaza sayar da shi wasu msu sayen sun saya akan bashi wadanda kuma suka siya sun tura kudin ne ta hanyar bakin ba wai gundarin kudin suka biya ba, inda hakan ya kara jefa masu samar da kwan a cikin matsala,inda ya yi kira da gwamnatin jihar da ta kawo masu dauki.
Hakan ya sa gwamnatin jihar ta fitar da sanawa ta hanyar kakakin yada labaran gwamnatin Makut Macham, inda gwamnatin ta saye sauran kwan ta kuma umarci masu kiwon su kais u kai tsaye zuwa ga gidajen marayu, makarantun gwamnati, asibitocin gwamnati don rabar da su kyauta.
Bagudu ya tabbatar da cika wannan umarnin na gwamnatin, inda ya sanar da cewa, bayan da kungiyar ta dauki kididdigar yawan kwan da ‘ya’yan suka samar, nan take suka cika umarnin na gwamtain jihar na tura kwan inda ta bayar da umarnin akai.
Sai dai, shugaban ya sanar cawa, har yanzu suna ci gaba da jiran gwamnatin ta tura masu kudaden na kwan da suka rabar, inda ya kara da cewa, wannan daukakin na gwamnain, ya taimaka masu domin farashin kwan ya fara karuwa a jihar.