Yau kimanin wata daya ke nan, da mummunan ambaliyar ruwan sama ta auka ma wasu sassan garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno,abinda yayi sanadiyar lalacewar kayan al’umma na miliyoyin Naira tare da mutuwar mutane da dama.
Annobar ta kuma yi awon gaba da daruruwan gonaki da lalata gidaje da dama, da wasu wuraren da ake gudanar da hada-hadar kasuwanci da dai sauransu.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara
Wasu kwararru sun danganta annobar, a matsayin wadda ta fi mafi muni a cikin shekara 30 da suka wuce, duba da yadda tun da farko, aka kiyasta ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 30.
Sai dai kuma, wasu rahotanni da ba a tabbatar da sahihancinsu ba a hukumance, sun ayyana adadin wadanda suka rasu da cewa sun zarce hakan.
Annobar ta shafi sama da miliyoyin mutane, wadda kuma aka samu labarin, ta raba mutane 414,000 daga matsagunan su.
Tun bayan aukuwar iftibla’in kungiyoyi na kasashen waje, gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi, manyan fitattu ‘yan Nijeriya da sauran wasu kamfanoni, suka bai wa gwamnatin Jihar Borno gudunmawar kudade da wasu kayan agaji, bisa nufin tallafa wa wadanda iftibla’in ya aukawa.
Wannan gudunmawar tasu, domin a taimaka wa wadanda iftibla’in ya shafa, abin yabawa ne.
Gwamnatocin tarayya da na jihohi sun dauki matakan gaggawa domin agazawa wadanda lamarin ya shafa, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda wadannan al’umomin suke ci gaba da jurewa jimirin kalubalen ayyukan ‘yan ta’adda da kuma na, ‘yan bindiga daji.
Gwamnatin jihar, ta kafa kwamitin, da zai yi nazarin iftibla’in wanda kuma zai ba gwamnatin shawara, a kan yadda za a yi gaggawar sake mayar da wadanda lamarin ya shafa, zuwa ga matsugunan su don ci gaba da rayuwa.
Tuni dai, gwamnatin ta samu gudunmawar kudi na Naira biliyan 7 daga cikin alkawuran da wasu masu taimakawa suka yi na bayar da ta su gudunmawar.
Wannan jaridar ta jinjina wa wadanda suka bada gudunmawar daga kungiyoyi na waje, da na cikin gida a kan tallafawa al’umomin da iftibla’in ya shafa.
Sai dai kuma, duk da irin wannan gudunmawar da suka bayar, tallafin bai isa ga wadanda lamarin ya shafa ba.
Idan aka yi la’akari da yadda aka samu raguwar ruwan sama, ya kamata mahukunta su gaggauta samar da tsarin sake mayar da wadanda lamarin ya shafa, zuwa ga matsugunan su.
A ra’ayinmu, aikin da ke gaba na bukatar yin kokari tare da samun hada kai.
Naira biliyan 7 da aka samu ta gudanmawar da aka bayar, da kuma sauran alkawuran kudi da aka yi, sun kai jimillar Naira biliyan 13, a saboda haka, ya zama wajibi ne a tattara wadannan kudaden yadda ya dace, domin sake gyaran matsugunan al’umomin da abin ya shafa.
A yayin da muke yin wannan rokon, muna kuma yin kira da ayi gyara yadda al’amuran ke tafiya a sansan da gwamnatin jihar ta bude a jihar, domin ajiye al’umomin da abin ya shafa, musamman ma yadda ake ganin ana sayar da wasu kayan da aka bayar domin taimakawa ‘yan gudun hijirar na ambaliyar ruwan.
Akwai babban nauyi a kan hukumomi na kare wadanda lamarin ya shafa, daga batagarin jami’an gwamnati, masu cin hanci, ta hanyar yin amfani da bazar wadanda ifitibla’in ya shafa.
A bangare daya kuma, gudunmawar kudaden da aka samu, ya zama wajibi ne, a yi amfani da su yadda ya dace, musamman domin wadanda abin ya shafa, su sake tsayawa da kafafunsu su kuma ci gaba da wata sabuwar rayuwa.
Kazalika ma, ta hannu daya kuma, muna yin kira ga wadanda suka yi alkawarin bayar da gudunmawar su ta kudi, da su cika alkwarinsu a kan lokaci, wanda hakan, zai ragewa wadanda iftibila’in ya shafa na radadin rayuwa.
A namu ra’ayin, shi ne sake giggina matsugunan al’ummomin da lamarin ya shafa don su koma su ci gaba da gudanar da kasuwancin su.
Wadannan matakan, na bukatar daukar inganttaun matakai na gajere da na dogon zango, duba da yadda al’ummomin da abin ya shafa sun zama tamkar sai sun sake wani sabon lale, na ci gaba da rayuwa, muna kuma kira, da a samar da shirin sake gina gidaje na wadanda suka rasa gidajen su, saboda iftibla’in.
Mun gamsu kokarin da gwamnatin Borno yake yi na taimakawa, bama kamar idan aka yi la’akari da tuni, ta fara yin abin da ya dace.
Muna bayar da shawarar cewa, ya kamata a hada wannan kokarin da ake yi, tare da bayar da tallafin yin sana’oin kasuwanci ga wadanda abin ya shafa.
Kazalika, kar a bar manoman da amfanin gonakan su ya lalace sanadiyar amlabiyar, domin suma suna da bukatar tallafa masu da Iri da sauran kayan aikin gona domin su sake komawa yin sana’arsu, ta noma.
Ya kamata, a samar da shirin gaggawa da kuma wanzar da shi, a kan lokaci, musamman ma domin sake gyaran kayan da suka lalace, ciki har da hanyoyi da sauransu.
Bisa bayanan da aka samu, shekarun da suka wuce, irin wadannan al’ummomin da ifibla’in ya shafa, ba sa samun kulawar da ta kamata.
A saboda irin wannan muna gargadin hukumomin bayar da agajin gaggawa kamar irinsu NEMA, a kan samar da daukin jeka na yi ka, wato kawai, kamar yadda suka saba yi, na rabar da Katifu, kwanukan rufi, ga wadanda wata annobar daban ta aukawa.
Maimakon hakan, ya kamata NEMA da gwamnati Borno, su hada karfi da karfe don samar da kwakkwaran shirin sake gina matsugunan alu’mmomin da abin ya shafa.
Nuna damuwar da kungiyoyin kasashen waje suka yi ga wadanda ifibla’in ya shafa, abin yabawa ne, muna kuma kira da a kara yawan fahimta.
Aikin sake mayar da al’ummomin jihar Borno,da iftibla’in ya shafa, na bukatar daukar matakan gaggawa da kuma yin amfani da kudaden da aka bayar na gudunmawa yadda ya dace.
Daukacin abin da ake bukata a yanzu shi ne, mayar da hankali a kan kalubalen tare da tabbatar da cewa, al’ummomin da iftibla’in ya shafa, gudunmawar ta isa gare su.