Rumbun samar da wutar lantarki na Nijeriya ya sake rugujewa, wanda ke zama karo na biyar a shekarar 2024.
Wannan rugujewar ta jefa ƙasa baki ɗaya cikin duhu, kamar yadda bayanan da ISO wani reshen kamfanin rarraba Wutar Lantarki na ƙasa (TCN), suka tabbatar.
- NLC Na Gudanar Da Zanga-zanga A Ofishin KEDCO Na Kano Kan Ƙarin Ƙuɗin Wutar Lantarki
- 1st Franklin Financial In Dahlonega, Ga 30533
Rumbun, wanda yake rarraba megawat 3,566 da misalin ƙarfe 6:00 pm na yamma, ya ruguje inda ya dawo zuwa 0.00 megawat da ƙarfe 7 na yamma, wanda ya haifar da katsewar wuta ga dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki 11.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya tabbatar da wannan katsewa, yana mai danganta shi da “matsala a tsarin” da ya faru da misalin ƙarfe 6:48 na yamma.
Kamfanin, a cikin wata sanarwa da Shugaban Sadarwarsa, Sani Bala Sani, ya sa wa hannu, ya bayyana takaici game da lamarin tare da tabbatar wa abokan huldarsa cewa ana kan ƙoƙarin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa.