Ranar 10 ga watan Disamba ita ce ranar kare hakkin dan Adam ta duniya, kuma ita ce ranar cika shekaru 76 da kaddamar da sanarwar kare hakkin dan Adam ta duniya. A gun taron manema labarai da aka saba yi a wannan rana, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin na dora muhimmanci kan mutunta da kare hakki dan Adam, tana mai dagewa kan sanya jama’a a gaba a yayin da take gudanar ayyukan bunkasa hakkin dan Adama wanda ya dace da yanayin zamani kuma ya dace da yanayin kasa. Kuma an samu manyan nasarori a yunkurin kare hakkin dan Adam.
Mao ta kara da cewa, “muna kira ga dukkan bangarori da su mutunta manufofi da ka’idojin Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya, da gudanar da tattaunawa mai ma’ana da hadin gwiwa a fannin kare hakkin bil Adama, tare da sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci a fagen kare hakkin bil Adama na kasa da kasa. Muna kuma fatan daidaikun kasashe za su yi watsi da tsarin diflomasiyya na tilastawa sauran kasashe bin tsarinsu, kuma su daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ta hanyar fakewa da batutuwan kare hakkin bil Adama.”
Bugu da kari, a martaninta ga Amurka na ikirarin cewa za ta kakaba sabbin takunkumin hana biza ga jami’an Hong Kong da ke aiwatar da dokar tsaron kasa ta Hong Kong, Mao Ning ta yi nuni da cewa, kakaba takunkumin hana biza kan jami’an Hong Kong ta hanyar batutuwan da suka shafi Hong Kong da Amurka ta yi, katsalandan ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, tare da matukar keta ka’idojin dokokin kasa da kasa da kuma muhimman ka’idojin dangantakar kasa da kasa. Bisa tanadin da suka dace na dokar hulda da kasashen waje ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin, da kuma dokar adawa da takunkumin kasashen waje na jamhuriyar jama’ar kasar Sin, bangaren kasar Sin ya yanke shawarar kakaba takunkumin hana biza ga jami’an Amurka da suka nuna halin rashin kyautawa game da batutuwan da suka shafi Hong Kong. (Mohammed Yahaya)