Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana damuwarsa kan yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa a Nijeriya, yana mai cewa yana rayuwa cikin bakin ciki a kullum saboda matsalar.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi wa ‘Yan Nijeriya a ranar Lahadi 12, ga watan Yunin 2022.
- 12 Ga Yuni: Muhimman Abubuwan Da Buhari Ya Fada A Jawabinsa Na Ranar Dimokuradiyya
- 2023: An Bukaci Tinubu Ya Dora Kan Irin Salon Mulkin Buhari Kwabo Da Kwabo
A yayin da yake tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnati na aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro, ya umarce su da su kasance masu yin addu’a.
“A wannan rana ta musamman, ina son mu sanya duk wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa cikin tunaninmu da addu’o’inmu’”
“Ina rayuwa kullum tare da bakin ciki da damuwa ga duk wadanda aka kashe da irin ta’addanci da garkuwa da mutane suke Yi,”
“Ni da jami’an tsaro muna yin duk mai yiwuwa don ganin mun kubutar da ‘yan Nijeriya da mutane marasa galihu,”
“Ga wadanda suka rasa rayukansu, za mu ci gaba da neman wa iyalansu hakkokinsu kan wadanda suka aikata laifin. Wadanda ake tsare da su a halin yanzu, ba za mu tsaya ba har sai an sako su, kuma an gurfanar da wadanda suka yi garkuwa da su a gaban kuliya. Idan muka hada kai, za mu ci nasara a kan wadannan ‘yan ta’adda.
“Mun gyara tare da zuwa da wasu tsare-tsare a bangaren tsaron tsaro. Wasu kadarorin tsaro da muka sayo shekaru uku da suka gabata sun iso kuma an tura su wuraren da suka dace.
“Ana inganta tsarin tsaron yanar gizonmu da tsarin sa ido don ƙara haɓaka ikonmu na bin diddigin abubuwan da suka aikata laifuka. Muna kuma daukar sabbin ma’aikata da horar da su a dukkan hukumomin tsaro da na leken asiri domin karfafa tsaron kasa baki daya.” Duk cikin Jawabin Shugaba Buhari.