• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A KUSKURA: Yadda Kayan Maye Ya Zama Ruwan Dare A Tsakanin Al’umma

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
A

Kwanan nan, an yi ta samun yaduwar wani kayan maye mai hatsarin gaske wanda aka fi sani da A kuskura/Kuskura ko Akurkura, wanda ake yin shi da Tumfafiya hade da ganyen wiwi da na ‘tobacco’ da wasu sinadarai, wanda kuma ya fi yaduwa a yankin arewaci da kudu maso yammacin Nijeriya. Wasu lokutan, Akuskura yana kai mutum ga gargarar mutuwa saboda tsananin karfin sinadaran da aka hada shi da su.

Sunan Akuskura, wanda a wasu lokuta ake kira kuskura ko akurkura, ya samo asali ne daga kalmar “kuskura” na Hausa. Ana amfani da sinadarin Akuskura ne ta hanyar kuskure baki a tofar, ko kuma a shaka a hanci. Da zarar an yi hakan, nan take yake fara aikin sa, inda yake gusar da hankali kai tsaye a mafi yawancin lokuta, da kuma kara kuzarin gabobin jiki, rudar da tunani da hana bacci. A wasu lokutan kuma yakan saka mutum ya shiga cikin mawuyacin hali na tsananin kishi da rikewar makogoro ko suma.

  • Hukumar NDLEA Ta Cafke Wani Basarake Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Sakkwato
  • NDLEA Ta Yi Nasarar Cafke Shahararren Dan Kasuwar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo A Abuja

A kwanan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama sama da kwalabe dubu bakwai na haramtacciyar sinadarin a hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda aka aika su zuwa jihohin Borno, Kano, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Gombe da Nasarawa. Duk da cewa wannan shi ne mafi girman kamu da akayi na sinadarin da akayi, akwai da dama da aka kama a wurare mabanbanta kafin shi.

Biyo bayan kamen da aka yi, babban daraktan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, a wata ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Abuja a ranar 19 ga watan Agusta, ta sanar da hana amfani da sinadarin a hukumance. Ta ce hukumar ta samu rahotanni da dama na amfani da Kurkura musamman a yankin Kudu maso Yamma da Arewacin kasar nan. Daraktan ta kara da cewa ganin hakan ne ya sa hukumar ta shirya taron manema labarai don kara tabbatar wa al’umma haramcin amfani da sinadarin kuskura, sakamakon illolin da take dauke da su.

Akuskura nau’in miyagun kwayoyi ne da ake kira sabbin sinadaran gusar da hankali, a turance (New Psychoactive Substance). NPS sinadarai ne wadanda yarjejeniyar 1961 akan kayan shaye-shaye da Yarjejeniyar 1971 na majalisar dinkin duniya basu ambace su a matsayin kayan shaye-shaye ba saboda a lokacin babu bullar su. Sai dai duk da cewa basa cikin jerin kwayoyi na wadannan yarjejeniya, NPS suna iya daukan illoli ga lafiyar jiki masu tasirin gaske. Wannan yana nuna cewa akuskura ya shiga nau’in miyagun kwayoyi, kamar yanda hukumar NAFDAC ta ayyana

LABARAI MASU NASABA

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Duk da cewa yana da illoli ga lafiyar dan Adam, kuma yana dauke da sinadaran maye da suka hada da wiwi da sauran su, Akuskura yana yawo a tsakanin masu sayar da maganin gargajiya a garuruwa daban-daban, musamman ma a cikin arewacin Nijeriya a matsayin magani, wanda kuma bincike ya tabbatar da cewa baragurbin kwaya ne.

Masu sayar da shi sukan yi ikirarin cewa yana maganin sanyi, mura, tari, ciwon kai, hawan jini, ciwon suga, karin kuzarin mazantaka, maganin amosani, maganin gajiya da dai sauran su.

A zahirin gaskiya, babu wani ingantaccen nazari da masana sukayi wanda suka samu yakinin cewa Akuskura na maganin ko da daya ne daga cikin wadannan cututtuka. Abun da bincike ya tabbatar shine; kuskura sinadari ne na kwaya wanda hukuma ta haramta amfani da shi.

Wannan kuwa yana nuna cewa duk mai sayar da Kuskura yana taka doka ne kuma zai iya gamuwa da fushin hukuma, haka ma wanda ya ke sha, da wanda yake safarar su, kamar yanda shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa ya ayyana a wani hira da yayi da gidan radiyon BBC Hausa, inda yace hukumar NDLEA ba zata saurarawa masu ta’amuli da sinadarin Akuskura ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abduljabbar
Labarai

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka
Manyan Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025
Next Post
Ya Kashe Yayansa Kan Kudin Wutar Lantarki Naira 1,500 A Anambra

Ya Kashe Yayansa Kan Kudin Wutar Lantarki Naira 1,500 A Anambra

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
Abduljabbar

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025
Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.