Akalla ‘yan Nijeriya 78 ne suka rasa rayukansu, yayin aka yi garkuwa da mutum 12 a fadin Nijeriya tun lokacin da Shugaban kasa Tinubu ya sha rantsuwar fara aiki.
Lamarin ya faru ne a jihohin Ribas, Zamfara, Kaduna, Ogun, Sakkwato da kuma Babban Birnin Tarayya.
- Hajjin Bana: Ku Zama Jakadu Na Kwarai – Gwamnan Gombe Ga Maniyyata
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 4, Sun Kwato Makamai A Jihar Zamfara
An samu wannan bincike ne daga masu bindiddigin sha’anin tsaron Nijeriya da ke da alaka da kasashen ketare.
Rahoton ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun halaka mutum hudu da kuma bille wa mutum biyu kawuna a Jihar Ribas a ranar 29 ga Mayu.
A ranar 30 ga Mayu kuwa, ‘yan bindiga sun kashe shugaban kungiyar sa-kai tare da wasu mutum 24 a Jihar Zamfara. Haka kuma a wannan rana ta 30 ga Mayu, an yi garkuwa da shugabannin matan jam’iyyar APC bayan sun halarci bikin rantsar da gwamnan Jihar Kaduna.
A dai wannan rana, ‘yan bindiga sun kasha wani mutum tare da yin garkuwa da matarsa da ‘ya’yansa guda hudu a Jihar Kaduna. Sannan kuma a wannan rana ta 30, wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun halaka mutum shida a Jihar Ribas.
A ranar 31 ga Mayu, ‘yan bindiga dadi sun kai hari a wata gona da ke Jihar Ogun, inda suka kashe mutum uku tare da yin garkuwa da mutum biyu. A Abuja kuwa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum hudu a ranar 4 ga Yunin 2023.
‘Yan Nijeriya suna cikin damuwa na ganin an yi musu maganin babbar matsalar da ta addabesu na kisan gilla da ake musu babu dare babu rana, wanda hakan ya janyo asarar yaruka da dama da kuma dimbin dukiyoyi sakamakon rashin tsaro. Ko Tinubu zai iya cimma burinsa wajen kawo karshen rashin tsaro a Nijeriya?