Kimanin mutum 15 ne suka rasu kuma mafiyawancinsu mata, da haihuwar jarirai akalla 35 a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Jibiya a Jihar Katsina, a cikin watanni uku da suka gabata.
Shugaban ‘yan gudun hijira Malam Sa’adu Salisu ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da tawagar ‘yan jarida masu aikawa da rahotanni daga jihar Katsina suka kai ziyarar gani da ido a sansanin da ke makarantar ‘yan mata ta jibiya.
Ya kara da cewa sun kai kimanin su dubu 16 da suka fito daga bangarori daban-daban da suka hada da Tsabu, Farfaru, Kwari da Garin Alhaji da Zango da Shinfida da sauran garuruwa da ke kusa da garin Jibiya.
Wadannan mutane dai sun rasa muhallansu ne sakamakon haren-haren ‘yan bindiga da masu satar jama’a domin neman kudin fansa kuma lamarin ya ki ci ya ki cinyewa.
Shugaban ‘yan gudun hijirar ya ce wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar basa kwana a sansanin sakamakon rashin wurin kwana mai kyau da rashin gidan sauro da lantarki da ruwan sha da sauran kayayyakin more rayuwa.
“Sannan muna fuskantar matsalar tsaro a wannan wuri, duk wannan yawan namu dan sanda biyu ne kawai ke tare da mu, sannan yanayin da muke ciki abin ba dadin ji musamman matsalar rashin abinci wadatacce.” In ji shi.
Haka kuma Malam Sa’adu Salisu ya kara da cewa lokacin baya suna samun abinci har sau uku a rana amma a hankali a hankali yanzu wani lokaci sau daya suke cin abinci. Ya kara da cewa wasu mutanen ma a kasa suke kwana saboda rashin isassun abin shinfida wasu kuma suna shinfida zannuwansu suna kwana a kai.
Game da matsalar rashin lafiya kuwa shugaban ‘yan gudun hijira ya ce suna samun gudunmawar magunguna daga gwamnati da kungiyoyi da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni
A cewarsa yanzu babban abin da ya fi damunsu shi ne yadda yaransu musamman mata kanana fiye da dubu uku ba sa zuwa makaranta saboda halin da suka tsinci kansu a cikin, inda ya ce lallai wannan matsala da ita suke kwana da ita suke tashi.
Da aka ji ta bakinsa, shugaban karamar hukumar Jibiya Hon. Bishir Sabiu Maitan ya ce duk abin da ‘yan gudun hijira ke bukata bakin gwargwado gwamnatin jihar Katsina na yi ba tare da wata matsala ba.
Hon. Maitan ya ce kullum sai an dafa buhun shinkafa goma sha biyar, kuma ya ce bashi da labarin cewa sau daya ake abinci a sansanin ‘yan gudun hijirar, domin gwamnati sau uku take ba da abinci.
Ya kara da cewa babu wata bukata da suka kai wa Gwamna Masari da bai yi masu ba, “saboda haka gwamnati na bakin kokarinta wajan kyautata wa ‘yan gudun hijira, sai dai ajizanci na Dan’adam ba za a rasa ‘yan kurakurai ba.” In ji shi.