Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya shiga siyasa ne domin yi wa al’umma hidima, ba don ya saci kudaden jama’a ba.Â
A lokacin da yake magana a wani shirin rediyo, ya jaddada cewa ya yana da rufin asiri tun kafin ya zama gwamna, kuma ya shirya yin rantsuwa da Alkur’ani don tabbatar da gaskiyarsa.
- Akpabio, Kekere-Ekun, Abbas Da Wasu Sun Samu Lambar Girmamawa ta Kasa
- Murnar Ƴanci: Gwamna Fintiri Ya Yafe Wa Fursunoni Biyu
Ya zargi Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da yi masa sharri kan zargin shi da mukarrabansa sun wawushe Naira biliyan 423 a lokacin da yake gwamna.
El-Rufai ya nuna takaicinsa kan zargin da ake yi masa da kuma farautar abokan aikinsa ta hannun hukumomin yaki da cin hanci.
Ya bayyana cewa ya bar al’amarin a hannun Allah, kuma bai damu da ya kare kansa a bainar jama’a ba.
Duk da kalubalen shari’a da yake fuskanta, yana ci gaba da harkokinsa na yau da kullum tare da ci gaba da yi wa al’umma hidima.
A nan gaba, El-Rufai ya bayyana cewa bayan ya kammala karatunsa, yana shirin dawowa harkar siyasa a shekarar 2027.
Ya sake tabbatar da kudurinsa na cigaba da yi wa jama’a aiki da kokarin bunkasa ci gaban jihar.