Zanga-zangar da ake yi a Nijeriya a halin yanzu, ta fara ne a ranar 1 ga watan Agusta 2024 kuma tana da dalilai da yawa wadanda aka yi nazari, sharhi da kuma ba da ra’ayoyi a kafofin watsa labarai da marubuta da yawa ciki har da wannan marubuci a yawancin ra’ayoyin nawa da suka shafi sassa daban-daban na Nijeriya.
Kuma zanga-zangar kamar za ta kara ruruwa idan ba a yi amfani da basira ba wajen tafiyar da lamarin ba.
- Muna Samun Nasarori A Yaki Da Gurbatattun Masana’antar Kannywood – Tijjani Asase
- Bayani A Kan Fitowar Jini A Dunkule Yayin Al’ada
Dalilan farko da na musamman masu yawa da suka haddasa zanga-zangar sun hada da cire tallafin man fetur, karin farashin man fetur, karancin man fetur, cire tallafin wutar lantarki, hauhawar farashin kayayyaki, karancin abinci, matsalar tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayan abinci, faduwar darajar Naira a kan duk wasu kudade na duniya, rashin ingancin cibiyoyin kiwon lafiya, rashin aikin yi, rashin kyakkyawan yanayin kasuwanci da sada zumunci. Haka nan akwai batun harajin da ya wuce kima, yawan kudin ruwa, rashin isassun muhali, bashin da ba a biya ba na kudaden fenshon ma’aikata masu ritaya na gwamnatin tarayya da na kananan hukumomi, sace-sacen mutane. da rashin tsaro, matsalar tattalin arziki, da sauransu na jefa miliyoyin mutane a Nijeriya cikin talauci mai dimbin yawa inda iyalai da dama ke kara kasa biyan kudin kiwon lafiya, sayen kayan masarufi na rayuwa da ingantaccen ilimi, wanda hakan ke kara jawo tabarbarewar tattalin arziki ga ‘yan kasa.
Bugu da kari, akwai rashin gamsuwa da manufofin gwamnati da ba su dace ba, kamar kusan kowane wata Gwamnatin Tarayya na neman Majalisar Dokoki ta kasa ta amince wajen karbo rancen biliyoyin daloli don amfanin ayyuka na alfarma, da aikace-aikacen da ba su da tasiri wajen tallafawa tattalin arziki, kamar kashe kudi kan kayayyakin alatu, gina gida na fiye da naira biliyan 19 ga mataimakin shugaban kasa, sayen sabbin jiragen sama na shugaban kasa wanda zai mayar da kasar baya da kuma wasu biliyoyin naira masu dimbin yawa na gyaran gidan shugaban kasa dake barikin Dodan da na mataimakinsa a Legas, da sayen manyan motocin alfarma na biliyoyin naira na fadar shugaban kasa da mazaunanta, da sayen sama da motoci kirar Toyota Prado jeep guda 300 a kan kudi kusan naira miliyan 160 kowanne wa ‘yan majalisa, da ware naira biliyan 6 domin gina wurin ajiye motoci ga ‘yan majalisar dokoki ta kasa.
Haka nan akwai sayen ayarin motocin ministoci da sauran masu taimaka wa shugaban kasa, ba da damar shigar da manyan sakatarorin ma’aikatu da shugaban ma’aikata a cikin tsarin IPPIS bayan sun yi ritaya, gina wani asibiti na daban na shugaban kasa da iyalansa, gina asibitin daban na ‘yan majalisar dokokin kasa, kashe kudi naira biliyan daya ko sama da haka don tattaunawa a kan mafi karancin albashi daga naira 30,000 zuwa naira 70,000 a halin yanzu, amma kuma albashi da alawus din masu rike da mukaman siyasa a kowane wata yana farawa ne daga naira 300,000 zuwa naira miliyan 30 ko sama da haka, da sauran wasu abubuwa na almubazzaranci duk da rashin wadatar kudade da ake ciki don jin dadin jama’a, da shelar cewa babu isassun kudade a cikin tattalin arzikin da za a magance matsalar tabarbarewan tattalin arzikin da talakawa ke fuskanta. A halin yanzu kuma bangaren zartarwa da na majalisa da kuma na baya-bayan nan bangaren tsaro suka ce wa ‘yan Nijeriya su ci gaba da hakuri a halin da ake ciki, dadin-da-dawa a kwanakin baya wani sanata ya fito ya ce za su zauna a Abuja su ci gaba da cin abinci. Wannan yana nuna maka irin tunaninsu da rashin kishi kasa!
Sanarwa
Masu zanga-zangar sun ba da sanarwar aniyarsu ta yin zanga-zanga daga 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga Agusta daga kusan farkon watan Yuli na shekarar 2024.
A halin yanzu, hukumomi maimakon mayar da hankali da yin abin da ya kamata, abin bakin ciki sun kare da karfin hali (wato courageous a turance). Ina mamakin me kalmar ke nufi a zuciyarsu!
Hakkin Masu Zanga-zangar
Shin zanga-zangar tana da madafa a dokan ce, a cikin turbar dimokuradiyya da kuma karkashin dokokin da suka dace na kasa da yarjejeniyoyin kasa da kasa?
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya 1999: Sashi na 38: Tabbatar da ’yancin motsi da ’yancin yin tafiya cikin walwala a cikin Nijeriya. Sashi na 39: Ba da garantin ‘yancin fadar albarkacin baki, ‘yancin daukar ra’ayi, karba da ba da ra’ayi ba tare da tsangwama ba. Sashi na 40: Yana ba da kariya ga hakkin yin taro da kungiyoyi cikin lumana, gami da hakkin kafa da shiga kungiyoyi.
Majalisar Dinkin Duniya: Sanarwar Hakkin Dan Adam ta Duniya (UDHR), 1948. Mataki na 19 yana kare ‘yancin fadin albarkacin baki, gami da ‘yancin neman, karba, da ba da bayanai. Mataki na 20 yana ba da tabbacin hakkin yin taro da kungiyoyi cikin lumana. A karkashin Alkawarin kasa-da-kasa akan Hakkokin farar hula da Siyasa (ICCPR), 1966. Mataki na 19 yana kare ‘yancin fadin albarkacin baki, gami da ‘yancin rike ra’ayi da ba da bayanai. Mataki na ashirin da daya ya ba da tabbacin hakkin yin taro cikin lumana. Mataki na ashirin da biyu yana kare ‘yancin yin tarayya.
A karkashin Yarjejeniya Ta Afirka Kan Hakkokin Dan Adam da Jama’a kuma Mataki na 11 ya ba da garantin ‘yancin yin taro ga kungiyoyi. Mataki na 9 ya kare ‘yancin fadin albarkacin baki.
Wasu Dokoki da Suka Dace:
Yarjejeniya ta Afirka kan Dimokuradiyya, Zabuka da Mulki, 2007: Inganta ka’idodin dimokuradiyya, ‘yancin dan adam, da bin doka. Sanarwa ta Majalisar Dinkin Duniya kan Masu Kare Hakkin Bil Adama, 1998 wanda yana kare mutanen da ke habakawa da ba da tallafi.
Don haka, idan aka sami sabani a Tsakani, Kundin tsarin mulkin Nijeriya da yarjejeniyoyin kasa da kasa (ICCPR, ACHPR) za su kasance a gaba a kan dokokin tarayya (Public Order Act, Dokar ‘Yan Sanda, Dokar Tsaro ta Kasa).
Me kalmar ‘#EndBadGobernanceInNigeria’ take nufi?
Kalmar tana nufin Kawo Karshen Mummunan Shugabanci wanda ya ci karo da sashe na 14 (2) (a) da ya bayyana cewa “mulkin jama’a na jama’a ne” da sashe na 16 (1) (a) da ke bukatar gwamnati ta “yi amfani da dukiyar kasa don amfanin al’umma ‘yan kasa”.
Rashin bin diddigin a aikin gwamnati: Shi kuma wannan ya saba wa sashe na 15(5) wanda ke bukatar gwamnati ta “dakile duk wata almundahana” da kuma sashe na 22 wanda ya “umurci kafafen yada labarai su rika bin diddigin gwamnati”.
Rashin gaskiya a aikin gwamnati: Ya saba wa sashe na 22 da ke bukatar gwamnati ta yi gaskiya a cikin harkokinta.
Munanan manufofin tattalin arziki da ke haifar da wahalhalu ga ‘yan Nijeriya: Ya keta sashe na 16 (1) (b) wanda ke bukatar gwamnati ta “tabbatar da mafi girman walwala, ‘yanci da farin ciki ga kowane dan kasa” da sashe na 17 (3) (c) wanda ya ba da umarnin gwamnati ta “jagoranci manufofinta don tabbatar da ‘yancin ‘yan kasa, su na rayuwa cikin aminci da kuma kyau”.
Abu nag aba shi ne rashin iya samar da tsaro ga ‘yan kasa da kuma kare ‘yan kasa daga masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi: Ya saba wa sashe na 14(2)(b) wanda ya bayyana cewa “tsaro da jin dadin jama’a shi ne babbar manufa da aikin gwamnati” da sashe na 33(1) wanda ke “tabbatar da hakkin rayuwa”.
Idan aka yi la’akari da bayanai dasu ka gabata, za a ga cin zarafin al’umma, mugunta, rashin tausayi, zalunci, rashin tausayi, bakin ciki da akalla dan Nijeriya miliyan 220 ke funskanta ga wahalhalu ko wace iri kuma yana kwatanta wadanda suka kira kansu zababbun shugabanni da wakilai a matsayin masu rashin hankali da kuma rashin sanin ciwon kai.
Dangane da Jawabin Shugaban Kasa
Jawabin Shugaban a takaice shine: Na ji ku, ina nan na dukufa cikin aiki,ku koma gida,tallafin mai an cire har abada,ku ci ga ba da hakuri kuma wannan zanza-zangar ta na da alaman siyasa a cikin ta.
Bugu da kari ya bayyana sanin halin ha’ula’i da tashe-tashen hankula a wasu jihohin kasar, ya kuma tabbatar da cewa akwai bukatar a samu kasa mai inganci da ci gaba.
Bayan haka sai ya yi shelar jadawalin kudaden da ya ce sun kashe wa jamaá kamar yadda aka ba da labari a kasidar gonar dabbobi (wato a turance labarin Animal Farm). Jawabin nasa ya kasance kawai kamar wasi-wasi ne cikin zuciyarsa da tirjiya!
Nasiha da Shawarwari
Masu zanga-zangar- Ku gudanar da muzaharar ku cikin kwanciyar hankali, babu kwasar ganima, ba fasa shaguna, ba cin zarafi, ba sata da dai sauransu.
‘Yan iska da masu daukar nauyinsu- Ku dena kutsawa cikin jerin gwanon masu zanga-zangar domin suna da goyon bayan doka da kuka rasa.
Ga masu barna da masu daukar nauyinsu- Ku dena amfani da yanayin don cin gajiyar ta da haddasa fitina.
Ga jami’an tsaro- Ku ci gaba da kasancewa marasa hanu a cikin siyasa, domin akwai kotun shari’a ta duniya, takunkumin kasa da kasa da kuma kungiyar kasa da kasa ta sabuwar duniya mai tafe (wato Multi-Polar World).
Ga jami’an gwamnati- Gwamnatoci da dama sun zo sun shude, wata rana kuma sai labari. Don haka a guji fitar da kalamai marasa kangado, barazana, batancin masu zanga-zanga da dakile zanga-zangar lumana da dai sauran su, sannan a saurari bukatun masu zanga-zangar,da ‘yan Nijeriya da abokan Nijeriya cikin hikima.
Kusan da cewa a dimokradiyya murya mafi rinjaye su ke da rana. (wato those against say nay, and the ayes habe it!).