Shugaban rundunar ‘yansanda na kasa, Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa, rundunar ta gano bindiga 182 da harsasai 430 a binciken da suka yi cikin wata daya.
Ganin wannan nasara da ‘yansandan suka samu ta gano wadannan makamai IGP din ya kara wa jami’an ‘yansandan karfin gwiwa kan su ci gaba da wannan aiki, domin gano bindigogin da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, musamman kafin ranar zabe.
- Dan Majalisar Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fita Yakin Neman Zabe A Bauchi
- EFCC Ta Gurfanar Da Farfesa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N1.4bn
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, CSP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a Abuja.
Kamar yadda ya ce, IGP ya umarci dukkan kwamishinonin ‘yansanda da su kara lura sosai wajen ganin ba a yi amfani da makamai ba lokacin da ake yin zabe mai zuwa.
Sannan kuma ya ce:“IGP ya tabbatar da cewa, an kama a cikin wata daya sun gano bindigogin da yanzu haka suke tuhumar wadanda aka kama da su, wanda kuma ya sha alwashin hukunta dukkan wanda aka same shi da bindiga ba bisa ka’ida ba.