Gobe Alhamis 4 ga watan nan na Mayu, rana ce ta matasan kasar Sin. Saboda haka, a cikin sharhin na yau, bari mu tattauna batun da ya shafi matasa.
Hausawa su kan ce “Karen bana shi ke maganin zomon bana.” Amma dai idan an yaudari matasa, za su iya fadawa kuskure. Misali, wasu matasan kasashen Afirka sun fara daukar ra’ayi maras kyau game da kasar Sin, sakamakon yadda suka yarda da labaran jabu, da wasu kafofin yada labaru na kasashen yamma suka watsa, ba tare da tantance gaskiyarsu ba. Sai dai kuma idan wadannan matasa sun samu damar hulda da kasar Sin da kansu, to, tabbas za su canza ra’ayinsu.
Cikin shekaru 20 da suka wuce, na gamu da matasan kasashen Afirka da yawa, wadanda suka kulla wata alaka da kasar Sin. Wasunsu na karatu a kasar Sin, wasu suna aiki a kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka, yayin da kuma wasunsu ke gudanar da ciniki tsakanin bangarorin Sin da Afirka, kuma dukkansu sun samu ci gaba sosai a harkokinsu.
A kwanakin baya na gamu da wata daliba ‘yar Najeriya a garin Jinhua dake gabashin kasar Sin, wadda ta taba koyon Sinanci a wata kwalejin Confusious dake Najeriya, sa’an nan ta samu kudin tallafin karatu don ta yi karatu a kasar Sin. Yanzu tana neman ci gaba da karatun digiri na 2 a kasar. Haka kuma, na tuna da wani saurayin da ya zo daga jihar Kano ta Najeriya, wanda na gamu da shi a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin wasu shekaru da suka wuce.
A lokacin yana zama a birnin Guangzhou, inda yake sayen kayayyaki masu alaka da wayar salula, yana tura su zuwa Najeriya a kai a kai. Ko da yake shekarunsa 20 da wani abu kacal a lokacin, amma ya riga ya mallaki wasu shagunan sayar da wayar salula guda 3 a wasu kasuwannin dake Kano.
Wadannan matasa da suka taba hulda da kasar Sin suna da wasu abubuwa na bai daya. Na farko, dukkansu suna kaunar kasar Sin. Sa’an nan na biyu, sun darajanta zumuntar dake tsakanin Afirka da Sin.
Saboda sun gane wa idanunsu ainihin yadda kasar Sin take, kana sun fahimci cewa, zumunta mai zurfi da hadin gwiwar da ake samu tsakanin Afirka da Sin, na ba su damar raya harkoki na kansu cikin nasara.
Mutanen da suka fahimci halayyar Sinawa sun san cewa, Sinawa na dora muhimmanci kan daukar hakikanin mataki. Saboda haka, idan kasar Sin ta dau niyyar kulla huldar abota tare da kai, to, ba za ta bar huldar ta tsaya kan maganar fatar baki ba kadai.
Wata babbar manufar kasar Sin ta fuskar hulda da kasashen Afirka ita ce, kokarin taimakawa kasashen Afirka wajen horar da matasa, ta yadda kasashen za su samu damar raya kansu.
Cikin wasu matakai guda 8 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin aiwatarwa, yayin da kasarsa ke hulda da kasashen Afirka, akwai horar da matasan kasashen Afirka don su samu fasahohin raya aikin gona na zamani, da dabarun da ake bukata domin wadatar da manoma, da koyar da ilimin sana’o’i daban daban ga matasan kasashen Afirka, da kafa cibiyoyin kirkire-kirkire, inda matasan Sin da Afirka za su iya hadin gwiwa da juna a kokarin kirkiro fasahohi, da bude sabbin kamfanoni, da dai sauransu. Duk wadannan matakai na tare da zummar taimakawa matasan kasashen Afirka samun kwarewar aiki, da wayewar kai, ta yadda za su iya raya kansu yadda suke bukata.
Ban da haka kuma, idan an duba yanayin da ake ciki a fannin tattalin arziki, za a san cewa kasar Sin na ba da muhimmiyar gudunmowa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kana tsare-tsaren tattalin arzikin Sin da na kasashen Afirka suna iya biyan bukatun junansu.
Saboda haka ana iya hasashen cewa, yayin da tattalin arzikin Sin ke kara samun ci gaba, da tabbatar da ingancin kansa, da neman zamanintarwa, kasar za ta haifar da karin damammaki na raya kai ga dimbin kasashen Afirka, gami da matasan kasashen. Yin amfani da damammakin da kyau, zai zame wa dumbin matasan kasashen Afirka, muhimmin dalilin da ya sa suke iya cika burikan da suka sanya a gaba.
Sai dai abun tambaya shi ne, wadanne ayyuka ne suka kamata matasan kasashen Afirka su yi kokarin gudanarwa a yanzu, ta yadda za su iya yin amfani da damammakin da kasar Sin ta samar?
A ganina za a iya fara da koyon Sinanci, da neman halartar ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar aikin ilimi, da halartar tarukan daukar ma’aikata na kamfanonin kasar Sin dake kasashensu, da dai makamantansu. Duk lokacin da ka fara kulla wata alaka da kasar Sin, to, ra’ayinka game da kasar, da shirinka kan rayuwa da aiki za su canza, cikin wani yanayi mai yakini. (Bello Wang)