Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rubuta wa majalisar dokokin jihar takardar neman amincewarta da kasafin kudin shekarar 2024 na karin kudi, N99, 221,503,569.90.
Bukatar gwamnan na kunshe ne cikin wata wasiƙa da aka karanta a zauren majalisar a yayin zaman da shugaban majalisar, Ismail Falgore ya jagoranta.
- Ambaliya Ta Yi Ajalin Mutane 49 A Arewa Maso Gabas – NEMA
- Gwamnan Nasir Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Naira Biliyan 6.5 Ga Mutane 65,000 A Kebbi
Yayin da yake karanta wasikar, Falgore ya bayyana cewa gwamnan yana neman amincewarsu ne bisa bin sashe na 122 (A da B) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan na 1999, don ƙara kaimi da aiwatar da ayyukan da suka sa gaba na inganta rayuwar al’ummar jihar.
Ya kuma bayyana cewa, daga cikin kasafin kudin, an ware kimanin Naira biliyan 34 na kudin ma’aikata da wata 35 na shirin ko ta kwana da kuma na sama da biliyan 31 don gudanar da ayyuuka.
Da yake zantawa da manema labarai bayan gabatar da wasikar ga majalisar, kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi na jihar, Musa Shanono, ya ce, kasafin farko na jihar na 2024 ya kai Naira biliyan 438 idan an hada da wannan karin kasafin da ake neman amincewa da shi a doka, zai kawo kasafin 2024 zuwa naira biliyan 537.
Yayin da yake nanata kudirin gwamnatin na mayar da hankali kan raya ababen more rayuwa da bunkasa walwala da ma inganta fannin lafiya da ilimi, Shanono ya jaddada cewa ƙarin kasafin kudin zai kunshi sabon mafi karancin albashi da dai sauransu.
Shi ma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Nassarawa Yusuf Aliyu, ya nemi goyon bayan sauran ‘yan majalisar don yin kira ga Gwamna Yusuf da ya gyara tare da sake gina filin wasa na Gwagwarwa da ke unguwar Gawuna a ƙaramar hukumar Nassarawa, don yakar ta’addancin da ake samu da safarar miyagun kwayoyi a filin wasan, da rashin tsaro a tsakanin al’umma.
A cewar Aliyu, mummunan halin da filin wasan ke ciki ya sanya wajen ya koma mafakar bata gari kuma abin tsoro ga mazauna yankin wanda gyara shi zai inganta tsaron al’umma.