Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, da ya biya diyya ga iyalan matafiya 16 da aka kashe a jiharsa yayin da suke dawowa daga Fatakwal don bukukuwan Sallah.
Gwamna Abba ya yi wannan kira ne yayin da Gwamna Okpebholo ya jagoranci tawagarsa zuwa Kano domin jajanta wa dangin mamatan da al’ummar Kano.
- Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
- Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
Ya ce yawancin wadanda aka kashe ‘yan Kano ne, kuma an kama su ne a Edo, inda aka yi musu azaba kafin a kashe su.
Ya yaba da ƙoƙarin Gwamnan Edo wajen kama waɗanda ake zargi da kisan, da kuma yadda aka gudanar da jana’izar mamatan bisa koyarwar addini.
Sai dai ya buƙaci a biya iyalan mamatan diyya cikin lokaci kuma a gabatar da waɗanda ake zargi ga jama’a don a tabbatar da adalci.
Gwamna Okpebholo ya bayyana takaicinsa kan lamarin, yana mai cewa tuni an kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za su fuskanci hukunci.
Bayan tattaunawa, Gwamna Abba ya jagoranci Gwamna Okpebholo zuwa ƙaramar hukumar Bunkure don jajanta wa iyalan mamatan.
Gwamnan Edo ya sha alwashin ganin an yi adalci ga mamatan da iyalansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp