Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin sarakuna masu daraja ta biyu guda uku na masarautun Rano, Gaya, da Karaye.
An sanar da nadin ne ta bakin mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana cewa sabbin masarautun za su kasance masu daraja ta biyu, yayin da masarautar Kano za ta kasance masarauta mai daraja ta daya.
- Dan Majalisar Tarayya Ekene Daga Kaduna Ya Rasu
- Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Sabbin Tuhume-tuhume Kan Ganduje Da Kwamishinansa
Sarakunan da aka nada sun hada da Alhaji Muhammad Mahraz Karaye a matsayin Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Isa Umar a matsayin Sarkin Rano, da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya a matsayin Sarkin Gaya.
Kafin nadin nasu, Alhaji Muhammad Mahraz Karaye shi ne Hakimin Rogo, Alhaji Umar shi ne Hakimin Bunkure, yayin da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya shi ne Sarkin tsohuwar masarautar Gaya.
Gwamna Yusuf ya taya sabbin sarakunan murna, ya kuma roke su da su zama masu rike al’adu, zaman lafiya, da hadin kan al’ummomin masarautunsu.
Gwamnan ya kuma rattaba hannu kan dokar kafa wadannan masarautun masu daraja ta biyu, wato masarautar Rano da ta hada da kananan hukumomin Rano, Kibiya, da Bunkure; Gaya ta hada da Gaya, Ajingi, da Albasu; sannan Karaye ta hada da Karaye da Rogo.
Sanarwar ta ce nadin ya fara aiki nan take.