An bude taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin-kan kasar Sin da kasashen Larabawa, a ranar 30 ga watan Mayu a nan birnin Beijing. Ana iya cewa, kasar Sin tana inganta ra’ayin zaman lafiya bisa ga hikimar da take da ita, kuma tana taka rawar jagoranci a fagen duniya.
Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 46, da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Libya. A yayin da yake tsokaci kan makomar dangantakar kasashen biyu a nan gaba, Dbeibah ya bayyana fatansa na ganin kasashen Sin da Libya sun kai ga zama abokai a fannin zuba jari, wanda hakan zai sa kasar Libya ta zama wata kofa ga kasar Sin ta shiga kasuwannin Afirka.
Har ila yau, Dbeibah ya jaddada cewa, kasar Sin tana ba da shawarar samar da zaman lafiya da bunkasuwa, da taimakawa kasashe masu fama da talauci a Afirka da sauran sassan duniya, kuma tana son karfafa tallafa wa wadannan kasashe a fannoni daban daban. A cewarsa, ba ma bukatar wadancan manyan kasashe masu karfi, wadanda ke jin dadin zaluntar talakawa, da kasashe marasa ci gaba sosai. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp