Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya mika takardar ajiye mukaminsa a daren ranar Lahadi, kamar yadda rahotanni suka tabbatar da hakan.
Wata majiya ta tabbatar wa da cewa Adamu, wanda ya zama shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar cikin watan Maris din shekarar 2022, ya aike da takardar murabus dinsa zuwa fadar shugaban kasa ta da ke Abuja gabanin dawowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu daga taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) a kasar Kenya.
- Rikicin APC: Kujerar Abdullahi Adamu Tana-kasa-tana-dabo
- Shugabancin Majalisa Ta 10: Hannun Agogo Na Neman Koma Wa APC Baya
Daya daga cikin majiyar ta ce Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya aika wasikar murabus din ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
Kazalika, wata majiya daga bangaren Adamu ta tabbatar da hakan, inda ta kara da cewa, “Shugaban Jam’iyyar APC na kasa ya yi murabus ne biyo bayan samun wasu bayanai na wasu mutane makusanta shugaban kasa da suke shirin tozarta shi a taron jam’iyyar da za a yi ranar Laraba.”
Sai dai majiyar ta musanta wani rahoto da ke cewa shugaba Tinubu ne ya bukaci Adamu ya yi murabus gabanin taron majalisar zartarwa na jam’iyyar na kasa da za a yi ranar Laraba. Jam’iyyar ta tsayar da ranakun 10 da 11 ga watan Yuli domin gudanar da tarukan kwamitinta na kasa da na NEC domin warware matsalolin da suka shafi rikicin kwamitin gudanarwar Jam’iyyar na kasa (NWC).
Sai dai daga baya an dage tarukan da aka shirya zuwa ranar Larabar nan.
Wani mamba a jam’iyyar ya ce, Adamun ya yi murabus ne a lokacin da ya bayanan shirin wasu mutane biyu masu fada a ji a kusa da shugaban kasar na shirin kulla masa tuggun siyasa da tozarta shi.
“Ya yi murabus ne saboda sun fara sanya hannu don tsige shi a tarurrukan Jam’iyyar da za a gabatar. Ya yi murabus ne domin ya tseratar da kansa daga wulakanci,” cewar dan Jam’iyyar
Da aka tuntubi Adamu, ya shaida cewa ba zai ce uffan ba kan lamarin har sai Shugaba Tinubu ya dawo daga taron AU.
“Ba zan yi magana kan wannan batun ba saboda shugaban kasa ba ya nan,” in ji Adamu
Idan dai ba a manta ba, tun da jimawa gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, Adamu ya ayyana tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar jam’iyyar a shugabancin kasa.
Wannan furuci da Adamu ya yi ya haifar da hargitsi a cikin jam’iyyar a wancan lokacin, yayin da gwamnonin jam’iyyar daga Arewa suka rufar masa suna masu nuna goyan bayansu game Tinubu.
Matsayin gwamnonin ya tilastawa jam’iyyar bude koffar neman tikitin takarar shugaban kasa ga kowa, inda Tinubu ya lashe zaben.
Ko a kwanakin nan an jiyo, Adamu na sukar jerin sunayen shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, kan sunayen da suka bayyana a matsayin shugabancin majalisun biyu.
Bayan faruwar lamarin, shugaba Tinubu ya gayyaci Adamu zuwa fadar fadar shugaban kasa, inda aka warware matsalolin a yayin zaman.