Farashin kayan abinci a Nijeriya na ci gaba da tashin gwauron zabi; wanda za a iya cewa, ba a taba ganin irin hakan a shekaru da dama da suka wuce a wannan kasar ba.
Wannan matsalar na faruwa ce a yayin da wasu manona har yanzu ke kan yin girbin amfanin gonakinsu. Babu shakka, hakan na ci gaba da jefa fargaba a zukatan masu ruwa da tsaki a kan yadda matsalar za ta yi wa fannin tattalin arzikin kasa illa tare da jawo rashin samar da wadatacen abinci a wannan kasa.
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas:Â Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
- Kamfanin Man Nijeriya Ya Sa Hannu Kan Fasahar Gano Sinadarin Methane
Sai dai, ba Nijeriya ce kadai ke fuskantar irin wannan kalubale ba, musamman ganin cewa kasar ta mayar da hankali ne wajen shigo da amfanin gona daga kasashen ketare kamar abin da ya shafi Rogo da Doya da sauran kayan abinci.
Kazalika, Nijeriya na fuskantar karancin abinci kamar Masara, Alkama da Waken Soya. Har ila yau, faduwar darajar naira a kasar ya kara tabarbara al’amura wajen shigo da kayan abinci cikin kasar.
Abin Da Ya Sa Farashin Abinci ke Tashi:
Wani bincike da aka gudanar a wasu manyan kasuwannin kasar nan da ake yin hada-hadar sayar da hatsi ya nuna cewa, duk da manoma sun girbe amfani mai yawa a noman da aka yi na bana, amma farashin kayan abinici na ci gaba da tashin gwauran zabi.
Misali a Jihar Katsina, farashin na ci ngaba da tashi; inda lamarin ke ci gaba da tayar wa da magidanta hankali, musamman ganin cewa, ana fara shirin shiga sabuwar shekarar 2024 ta fara yin wani noman.
Wani dilan sayar da hatsi a Jihar Kano, Alhaji Sa’adu Abashe ya yi nuni da cewa, akasarin mutane ba su da masaniya a kan abin da ke jawo tashin farashin amfanin gonar da aka noma na bana.
Sannan, ya danganta tashin farashin a kan faduwar darajar naira da tsadar takin zamani da kayan aikin noma da kudaden da ake biyan ‘yan kwadago da tsadar farashin man fetur da kuma kudin da manoma ke kashe wa domin yin jigilar amfanin da suka noma daga gonakinsu zuwa kasuwanni don sayarwa.
Sa’adu ya kara da cewa, farashin Masara, Dawa, Waken Soya, Gero da kuma Shinkafa ya yi matukar karuwa, inda kowane buhu daya mai nauyin kilo 100 ya kai kimanin naira 30,000.
Shi kuwa wani babban dan kasuwa a kasuwar Dandume da ke a Jihar Katsina, Alhaji Muhammad Salisu ya sanar da cewa, gannin yadda a bara masu sayen hatsi suna boyewa, don sayar da shi da tsada sun samu makudan kudade, hakan ne ya sa wasu masu kudin su ma suka sayi amfanin gonar da dama da aka noma a bana; suka boye domin samun kazamar riba.
Ya ce, wadanda suka sayi duk buhun Masara daya a kan naira 18,000 zuwa Naira 22,000, yanzu suna sayar da duk buhu guda kan akalla naira 55,000.
Shi kuwa Shugaban Kaungiyar Manoma Reshen Jihar Kano (AFAN), Malam Abdulrasheed Magaji Rimingado, ya danganta tashin farashin ne kan yadda wasu kamfanoni da ke sarrafa amfanin gonar zuwa wasu nau’ikan abinci ke yin rige-rigen saye amfanin da kuma tsadar jigilar amfanin gona.
A Jihar Neja kuwa, ‘yan kasuwa da manoma a jihar sun dangata tashin farashin a kan yadda ake yawan bukatar amfanin gonar. Shugaban masu sayar da hatsi a kasuwar sayar da hatsi ta Lemu a Karamar Hukumar Gbako, Alhaji Danladi Kowangi cewa ya yi; farashin buhun Shinkafar da ake nomawa a kasar nan ya tashi daga naira 22,000 zuwa naira 26,000, duk kuwa da cewa manoman sun jima da girbe Shinkafar.
Kowangi ya kara da cewa, sannan duk buhun Masara guda a halin yanzu, ana sayar da shi a kan naira 35,000, inda kuma ake sayar da buhun Gero a kan naira 35,000 a wannan kasuwa ta Lemu.
Har ila yau, a kasuwar Batati da ke Karamar Hukumar Labun a jihar da ake samun kayan abinci a cikin rahusa, ana sayar da duk buhun Dawa a kan naira 30,000, Gero naira 23,000, sai buhun jan Wake kuma a kan naira 40,000 zuwa naira 45,000.
A Karamar Hukumar Saminaka da ke Jihar Kaduna kuwa, shugaban masu sayar da hatsi a kasuwar, Manu Isah Idris ya danganta abubuwa da dama da suka jawo ci gaba da tashin farashin a daidai wannan lokaci; daga cikinsu a cewar tasa akwai batun yakin da ake ci gaba da yi a Kasashen Ukraine da kuma Kasar Falasdin tare kuma da cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayya ta yi.