Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur masu zaman kansu na Kasa (IPMAN), Alhaji Abubakar Maigandi Shettima Garima, ya bayyana dalilin da ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin man fetur suka gana domin tattaunawa da karamin ministan albarkatun mai Sanata Heineken Lokpobiri.
Garima a hirarsa da manema labarai a Kaduna ya sanar da cewa, ta gudanar a Abuja, wadda kuma aka samu sakamako mai kyau da zai kara amfannin fannin na sanar da wadataccen man a fadin kasar nan.
- Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha
- Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha
Shugaban wanda ya bayyana jin dadinsa a kan samakon tattaunawar, ya sanar da cewa, minitan ne, ya shiya taron tattaunawar da masu ruwa da ban da ban a fannin mai.
A cewarsa, an gudanar da tattaunawar ce, musamman kan yadda za a kara ingnata ayyukan masu ruwa da tsakin, don a samar da sakamako mai kyau a fannin.
Ya ce, a lokacin ganawar, an tattaunawa kan yadda za a lalubo da mafita kan matsalolin da fannin ke fuskanta.
A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai.
Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen man da sauki daga gun matatun main a Dangote da kuma na MRS.
A cewarsa, a yanzu haka ‘ya’yan IPMAN na yin dakon man daga gun wadannan matatun biyu, ba tare da matatun sun yi masu karin farashin man ba, inda ya shawarci sauran ‘ya’yan kungiyar da su je su yi rijista da wadannan matatun, domin su rinka sawo man da sauki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp