Wasu kananun masu sayar da kayan masarufi kamar Doya, Masara da sauran makamantansu a Jihar Kaduna sun bayyana cewa, ci gaba da samun karancin kudaden shiga a wurin abokan cinikayyarsu da kuma samun hauhawar farashin kaya a fadin wannan kasa, ya sa abokan cinikayya ba sa iya sayen kayan nasu.
A hirarsu da LEADERSHIP Hausa a Kaduna sun bayyana cewa, saboda karancin kudade a hannun jama’a, hakan ya sa suke tabka asara wajen rashin samun kudaden shiga.
- Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Kolin CEO Na APEC
- Yadda Gwamna Nasir Idris Ya Daura Damarar Bunkasa Ilimi A Jihar Kebbi
Daya daga cikinsu, Kabiru Sani da ke sana’ar sayar da Masara a Kasuwar Kawo da ke a jihar ya bayyana cewa, hakan na jawo musu matukar koma baya a sana’ar tasu.
Shi ma, wani mai sayar da Garin Kwaki; Auwal Muhammad ya sanar da cewa, yawan abokan cinikayyar da yake samu a baya, sun ragu sosai.
Ya danganta hakan, a kan rashin samun wadatattun kudade a hannun jama’a, inda ya kara da cewa; ga dai amfanin gona da dama a kasuwar, amma muna fuskantar kalubalen samun abokan cinikayya na yau da kullum.
Ita kuwa, wata mai sana’ar sayar da Doya a kasuwar Bakin Dogo; Hadiza Lawal ta sanar da cewa, ci gaba da samun hauhawar farashin kaya a kasar nan, ya jawo wasu abokan cinikayyarsu ba sa iya sayen Doyar duk da cewa, tuni sabuwar Doyar da aka noma a kakar noma bana na da yawa, inda ta kara da cewa; duk da karya farashin Doyar, abokan cinikayyar ‘yan kalilan ne ke iya saya.
Shi ma, wani karamin dan kasuwa mai sana’ar sayar da Dawa, Abdulrahim Abdullahi ya sanar da cewa, abokan cinikayyarsu sun yi matukar ragu.
A cewar Abdullahi, jama’a a halin yanzu ba sa iya sayen kaya kamar a baya, inda ya ce; idan abokin ciniki na da burin sayen misali mudu biyar, yanzu bai fi ya sayi mudu biyu ko uku ba; saboda tashin farashin da Dawar ya yi.
Shi ma, Muhammad Giyade mai sana’ar sayar da buhunhunan Shinkafa ya ce, tsadar ta sa ba ya samun abokan ciniki da dama; sabanin yadda yake samu a baya.
A cewarsa, hakan ya jawo rashin samun riba mai yawa da kuma rashin sayar da kayan da dama.