• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Na Sa Dokar Ta-ɓaci A Sashen Ilimin Jihar Zamfara – Gwamna Dauda Lawal

by Leadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa koma-bayan da aka samu a harkar ilimin jihar a baya ta sa ya ayyana dokar ta-ɓaci a sashen.

Ya kuma nunar da cewa ilimi wani ginshiƙi ne mafi muhimmanci ga ci gaban jihar Zamfara.

A Larabar nan ne ɗaliban makarantar ‘Leadsprings International Schools’ suka karrama Gwamna Lawal a gidan gwamnati da ke Gusau.

Kamar yadda yake ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana cewa waɗannan yara sun kuma miƙa wa Gwamnan wasu buƙatu guda bakwai masu muhimmanci, waɗanda su ke sa ran cimma a nan gaba.

Malam Idirs Bala ya ce, waɗannan tsammani da ake son cimma a aƙibar Zamfara, sun haɗa da babban birnin jihar, Gusau; sashen kiwon lafiya; harkar jiragen sama na Zamfara; fasaha; noma da sashen tattalin arziki, masana’antu da kamfanoni.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Cikin jawabin da ya yi wa waɗannan yara, Gwamna Dauda ya ƙara jaddada aniyarsa ta yin garambawul a harkar ilimi a jihar.

Gwamnan ya ce, “Ilimi ne abu na ɗaya cikin muhimman abubuwan da gwamnatina ta sanya a gaba, na biyu kuma, shi ne harkar tsaro. Sai dai harkar ilimin mu ba ta tafiya yadda ya kamata a lokutan baya. A kowane lokaci jihar Zamfara tana zamowa ta ƙarshe a harkar ilimi, wannan ne ya sa na sanya dokar ta-ɓaci a harkar ilimin.

zamfara

“Matakan sun haɗa da ɗaukar ƙwararrun Malaman da suka cancanta, samar da gine-gine da isassun kayan aiki, tare kuma da samar da hanyoyin koyarwa irin na zamani.

“Gwamnatina ba za ta gajiya ba, wajen sake fasalin harkar ilimi, ta yadda zai biya buƙatun al’ummarmu.

Daga nan kuma sai Gwamnan ya nuna jin daɗin sa bisa irin misalin ingantaccen ilimin da yaran suka nuna masa sun samu a makaranar tasu. Ya kuma gode wa Hukumar wannan makaranta ta ‘Leadsprings International School’ bisa wannan karramawa da suka yi masa.

zamfara

“Na ji daɗi da ganin irin yanayin karatunku da kuka nuna mana, wannan ya na nuni da cewa ɗaliban makarantar ‘Leadsprings International School’ a shirye suke su goga kafaɗa da kowa a faɗin duniyar nan.

“Ina godiya da wannan karramawa. Gwamnati na za ta ƙarfafa maku a duk inda za ta iya. Ina kira ga sauran makarantu masu zaman kansu su kwaikwayi wannan kyakkyawan aiki na ku.

Cikin nasa jawabin sa, mai makarantar ‘Leadsprings International School, Danjuma Sule ya bayyana cewa makarantarsa a shirye ta ke ta tafi da tsarin ilimin gwamnatin jihar Zamfara.

“Muna jinjina ga gwamnatin ka bisa irin jajircewarta wajen samar da yanayin karatu mai kyau a duk faɗin jihar. Muna kuma godiya da aniyar ka ta ɗaukaka ilimin mata a jihar. Yanzu haka, makarantar ‘Leadsprings International Schools’ muna da ɗalibai mata 386 a ajujuwa daban-daban, kuma muna nan muna nuna masu hanyoyin da za su zama masu amfani ga ci gaban Zamfara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Amurka

"Tutar Dimokuradiyya" Da Kasar Amurka Ta Rike Ta Lalace

LABARAI MASU NASABA

Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
zamfara

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.