ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Tutar Dimokuradiyya” Da Kasar Amurka Ta Rike Ta Lalace

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Kasar Amurka kullum tana rike da “tutar Dimokuradiyya” a hannunta, don neman ba da umarni ga sauran kasashe, ko da yake “tutar” ta riga ta lalace, har ta zama tamkar tsumma, sakamakon matakan da kasar ta dauka masu sabawa ruhin Dimokuradiyya.

Domin yi muku karin haske, zan dauki batun korar sojojin Amurka da kasar Nijar ta yi a matsayin misali. Cikin sauki ana iya fahimtar ra’ayin gwamnatin sojojin jamhuriyar Nijar, wato wa zai iya hakuri da wani “malami” mai girman kai, da ya zo gidanka musamman ma domin yi maka lakca kan tsarin Dimokuradiyya?

  • Xi Jinping Ya Nanata Wajibcin Yin Kwaskwarima Da Kirkire-Kirkire Cikin Hakikanin Hali A Lardin Hunan
  • Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Ingiza Ci Gaban Yankin Tsakiyar Kasar Sin

Ko da yake Nijar ta riga ta yi alkawarin dawo da aikin tsarin mulkin kasar cikin sauri, amma duk da haka, Amurka ta matsa mata lamba, da neman tsoma baki cikin harkokin kasar na diplomasiya, gami da ci gaba da girke sojoji a kasar don tabbatar da “komawarta kan turbar Dimokuradiyya”. Shin wane ne zai iya hakuri da hakan?

ADVERTISEMENT

Kasar Amurka ta dade tana kallon kanta a matsayin “shugabar kasashe masu Dimokuradiyya”, wadda ke da ikon saka ma sauran kasashe take na “mai Dimokuradiyya” da “mai mulkin kama-karya”, sa’an nan ta matsa wa “masu mulkin kama-karya” lamba da saka musu takunkumai. Ban da haka, kasar na kokarin kulla kawance na kasashe “masu Dimokuradiyya”, don neman mayar da sauran kasashe saniyar ware. Wannan mataki tamkar manufar wariya a fannin harkar siyasar kasa da kasa ne.

A kan samu wasu matakan wariya a duniyarmu, sakamakon yunkurin kasar Amurka na raba kawunan kasashen duniya. Misali, a kwanan baya, kasar Amurka ta sake gudanar da “taron koli na Dimokuradiyya”, wanda kasar Koriya ta Kudu ta karbi bakuncinsa a wannan karo. Ko da yake wurin da aka yi taron na kusa da kasar Sin da kasar Rasha, amma ba a gayyace su ba. Maimakon haka, an gayyaci jami’an yankin Taiwan na kasar Sin, wanda ba shi da ikon hulda da sauran kasashe a matsayin kasa. Ganin wannan matakin da aka dauka ya sa mutum fahimtar ma’anarsa ta tsokana, shi ya sa wani mai sharhi dan kasar Ghana mai suna Yirenkyi Jesse ya rubuta cikin wani sharhinsa a jaridar “Standard” ta kasar Kenya cewa “taron kolin Dimokuradiyyar a hakika bai nuna ra’ayin Dimokuradiyya ba ko kadan. Ban da haka an ga ya nuna girman kai na kasar Amurka, da manufarta ta raba kafa dangane da batun dimokuradiyya. ”

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Sai dai matakan kasar Amurka su kan sa mutanen duniya mamaki, da son sanin dalilin da ya sa kasar ke kallon kanta a matsayin mai ikon nuna yatsa ga sauran kasashe.

Mene ne yanayin da ake ciki a fannin tsarin Dimokuradiyya, cikin gidan kasar Amurka? Bisa binciken ra’ayin jama’a da kafar watsa labarai ta kasar Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar a kwanan baya, kan wasu mutane 39315 daga kasashe 32, kashi 71.1% na mutanen na ganin cewa, akwai dimbin kuskure cikin tsarin siyasar kasar Amurka, wadanda suka sabawa ruhin Dimokuradiyya, kana tsarin Dimokuradiyya mai salon Amurka ya haddasa wa kasar matsaloli irinsu: Masu hannu da shuni na mallakar ikon mulki, da rashin dabarar daidaita harkokin zaman al’umma, da samun rarrabuwar kawunan jama’ar kasar, da rashin imani kan gwamnati, da dai sauransu.

Kana sakamakon binciken ra’ayin jama’a da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka gudanar a kasarsu, shi ma ya nuna ra’ayi kusan iri daya ne, inda kimanin kashi 2 bisa 3 na jama’ar kasar Amurka da aka yi musu tambaya, suka ce gwamnatin kasar ta kasa wakiltar ra’ayoyin jama’ar kasar, a dimbin matakan da ta dauka masu alaka da tattalin arziki, da bakin haure, da shawo kan bindigogi, da dai sauransu.

Sa’an nan a fannin harkar kasa da kasa, ko da yake kasar Amurka ta lakabawa kanta “mai kare Dimokuradiyya a duniya”, amma hakika ba ta taba amincewa da matakan Dimokuradiyya ta fuskar al’amuran kasa da kasa ba. Maimakon haka ta rungumi manufar “kashin dankali”, daidai kamar yadda sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya fada a taron tsaro na Munich da ya gudana a kwanan baya, inda ya ce “Ta fuskar al’amuran kasa da kasa, idan ba ka zama mai cin abinci ba, to, mai yiwuwa ka zama abincin da za a ci. ” Wannan manufar ta haifar da dimbin wahalhalu ga sauran kasashe, duk lokacin da Amurka ke neman “kare Dimokuradiyya” a duniya. Za a iya tambayar mutanen kasashen Iraki, da Libya, da Afghanistan, da Sham, ko sun yarda da matakan kasar Amurka na yayata tsarin Dimokuradiyya a kasashensu? Ai kun san ba zai yiwu ba.

Hakika Dimokuradiyya wani abu ne da dukkan mutanen duniya ke daukakawa da darajanta. Akasarin kasashen duniya suna kokarin raya Dimokuradiyya, da neman tabbatar da shi a gidajensu. Saboda haka, kowanensu na da wani tsari na kansa, maimakon a ce akwai wani daidaitaccen tsarin Dimokuradiyya daya tak a duniya.

Dangane da ruhin Dimokuradiyya, na ga yadda masana na kasashe daban daban suka rubuta bayanai kusan iri daya, wadanda suka shafi kasancewar tsare-tsaren Dimokuradiyya daban daban, da girmama mabambantan ra’ayoyi, da kokarin samar da alfanu ga dan Adam, da dai sauransu. Don haka bisa kalamansu, za mu iya gane cewa, “tutar Dimokuradiyya” da kasar Amurka ta rike ta riga ta lalace sosai, har ma ba za iya gane yanayin ta ba. (Bello Wang)

Amurka
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Sace Direba Da Fasinjoji 18 A Katsina

'Yan Bindiga Sun Sace Direba Da Fasinjoji 18 A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.