Bidiyoyin da tsohuwar uwargidan fitaccen jarumin nan, Adam A. Zango, AMINA UBA HASSAN, ke dorawa a shafukan sada zumunta da ke nuna tana rungumar danta, Haidar tana wakokin soyayya da shi sun yi matukar tayar da kura kwanan baya a shafukan. Wakiliyarmu, RABI’AT SIDI BALA ta tattauna da Amina, wacce ita ma fitacciyar jaruma ce da ke taka rawa a a cikin shiri mai dogon zango na ‘Labarina’, inda ta kawo hujjojinta na yin hakan. Har ila yau, tattaunawar ta yi waiwaye a kan zamansu da tsohon mijinta da kuma bayan rabuwarsu.
A Karanta hirar har zuwa karshe don jin yadda ta kaya:
Da farko za ki fara fadawa masu karatu cikakken sunanki…
Da farko dai sunana Amina Uba Hassan, an fi sanina da Maman Haider, a yanzu kuma mutane sun fi sanina da Jamila Labarina.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni kuma na girma a garin Kaduna, nayi firamare dina a Kaduna ‘National Teachers Instute”, daga nan na tafi ‘Secondary School’ a ‘Kueen Amina College’ ‘boarding school’ ce a kaduna. Bayan na gama sai na tafi nayi ‘Polytechnic’ dina a kaduna na karanci ‘Business Administration’, yanzu ina HND 2 a Polytechnic dake cikin garin Kano.
Idan na fahimce ki kina so ki ce a yanzu kina ci gaba da karatu kenan?
Eh! Ina ci gaba da karatuna dan yanzu ina ‘final Year’ dina na HND 2.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar kannywood, musamman yadda mutane suka saba ganinki a soshiyal midiya kwatsam aka ganki kin fito matsayin jaruma mai taka rawa a masana’antar Kannywood, me za ki ce a kan hakan?
Shiga ta cikin masana’antar kannywood zan ce Allah ne ya nufa na shiga, sabida gaskiya shekarun baya da suka wuce ban taba kawo hakan ba, dan ina kallon fim kamar zan iya zama na rika fatan ni ma zan zama ‘actress’ kamar haka, kamar Rani Mukherji da nake so ‘yar indiya kamar dai ‘on my own’ dai ‘yes something like she none’ zan iya yi amma shigowa ta masana’antar kannywood kawai sai dai na ce Allah ne yayi ba ni nayi ‘planning’ din shi ba.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Gaskiya ban samu wani gwagwarmaya ba zan iya cewa shiga ta kannywood ya zo mun da sauki, Kannywood famili ne ba yanzu na sansu ba, na sansu tuntuni saboda na zauna da sanannan mutum na kannywood ko na ce na auri mutumin da aka sani sosai a kannywood, shi ya sa ban samu wani gwagwarmaya ba gaskiya.
Sai dai abu daya shi ne ‘producers’ sun so su yi aiki da ni amma ganin yadda suke tare da shi wasu na ganin kamar sun ci masa fuska, nuni da yadda kamar ya nuna baya so, Allah dai ya yi da daukaka ta a cikin masana’antar kannywood sai bayan nayi ‘Gidan Danja’ kenan kwatsan kuma sai Allah ya kawo Malam Saira a rayuwata har yayi ‘offering’ dina wannan rol din da yau ya zama sanadinsa duniya sun sanni, amma ba wata gwagwarmaya.
Lokacin da za ki fara sanar da iyayenki kina son shiga cikin masana’antar domin zama jaruma, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Eh! to, da yake ni marainiya ce iyayena sun rasu, kannena biyu kadai gare ni wanda yanzu suna gidan mazajensu sun yi aure. A inda na samu kalubale shi ne wurin ‘Sisters’ dina sabida yadda suke ganin ana zagin ‘yan fim shi ya sa suka ji tsoro da farko, bayan na fara suka ga karbuwar abun, sai suka kyale, yanzu sun ba ni goyon baya dari bisa dari. Amma dai na samu ‘problems’ da su kuma ‘reason’ dinsu abu ne wanda ni ma nayi musu uzuri da haka, ba wanda zai so a ce ana zagin dan’uwansa a social media ko makamancin haka, kuma a yanzu suna yi mun fatan alkhairi a gabadaya rayuwata.
Ta bangaren tsohon mijinki Adamu Zango fa, shin kin samu wani kalubale daga gare shi game da hakan ko kuwa?
Eh! ta bangaren tsohon mijina na samu kalubale sosai gaskiya dan ba ya so, kawai ba yadda zai yi ne amma ba ya so, amma farkon da zan fara fim shi na fara yi wa magana, har ya ba ni karfin gwiwa ya nuna mun cewa in dai na mayar da ita sana’a to, idan kuma na mayar da ita wani abu daban to, shi ma haka zai zo mun.
Kawai na rike mutuncina, na rike mutuncin dana, da iyayena da suke kasa, shawara dai da yawa ya ba ni ranar dana fara fada masa, daga baya kuma ban san me ya gani ba, ban san me ya ji ba, sai ya zo ya nuna ba ya so, amma abin da Allah ya nufa ya ce zai faru sai ya faru ko mutum yana so ko ba ya so, sai kuma Allah ya sa dai a hakan mutane za su sanni, ba social media kadai ba Kannywood ma za su sanni.
Lokacin da ya nuna ba ya so kafin ki fara fim din ne ko kuwa bayan da ki ka fara ne, kuma ya ki ka ji a lokacin da ya nuna baya so, shin kin so ki bari din ko kuwa hakuri kawai kika ba shi?
Kafin na fara na yi masa magana a lokacin ne ya rika ba ni shawara har ya nuna mun cewa shi kansa zai ‘guiding’ dina da dai sauransu. To, daga baya ne bayan na zo na fara tafiyar Yahaya Bello Wali wanda Abdul Amat me kwashewa yake jagoranta tun a lokacin ya fara nuna ba ya so har yanzu ma dai, kawai dai ba yadda zai yi ne amma har yanzu a zuciyarsa ba ya so.
Kuma a lokacin da muka yi maganar da a ce bai ba ni karfin gwiwa ba, da ya kawo mun wasu illolin da wani abun ‘may be’ a lokacin zan iya amma kwarin gwiwar da ya ba ni a lokacin shi ya kara sa ban damu ba, sai daga baya kuma na fara ganin canji, kuma yanzu na riga nayi nisa na saba da aikin ‘like acting’ yanzu ya zama ‘part of my life’, ‘because’ abu ne wanda na san zan iya yin shi kowane irin rol aka ba ni zan iya taka rawa a kai, daga baya ne ya nuna baya so, amma yanzu nayi nisa maganar fasawa ma bai taso ba.
Ba ke ganin rashin son da yake yana yi ne sabida yaronsa da yake hannunki?
A’a! Dalilai shi kadai ya bar wa kansa sani yarona ba a hannuna yake ba hutu yake zuwa gurina, idan suka tafi tun da ‘boarding school’ yake lokacin ta kwana yake, idan ya dawo hutu kamar idan ya yi kwana 3 gidansu idan ba na nan yakan yi sati a gidansu to, idan ya zo gurina ba ya komawa sai idan kamar ana saura kwana 3 ko 2 ko ana gobe ma za su koma makaranta kafin ya koma gidan mahaifinsa, ba a hannuna Haidar yake ba, yana hannun babanshi kawai hutunsa ne gaba daya a guri na yake idan dai har ina nan to, yana dawowa hutu yana dan yin kwanaki kadan a gidan baban, zai tattaro kayanshi ko kuma na sa a je a dauko shi a kawo shi wajena, to komawa sai idan suna gab da komawa makaranta.
Me za ki ce dangane da maganganun da mutane ke yi cewa bai dace ba ki rika rungumar dan cikinki kina wakokin soyayya a social media?
To, wannan matsalarsu ce dan ni ba matsala ba ne a guri na, dana ne da na haifa, ni na dau cikinsa, na yi laulayi kamar zan mutu dan gabadaya cikin Haidar rainon cikin da na yi zan iya cewa na yi shi ne ni kadai, saboda a lokacin ne shugaban masana’antar kannywood ya rufe mahaifinshi a ‘prison’ tun cikin Haidar na da wata 3, bai fito ba sai da cikin Haidar ya kai wata takwas ne ko tara, idan ban manta ba ya kusan wata biyar ko shida a ‘prison’.
Ni na san wahalar da na sha, ni na san laulayin da na yi, ni na dauki cikin dana, ni na yi nakudar abuna, na haifi abuna, ni na kula da abuna, dan sai da ya kai shekara biyu mahaifinshi ya karbe shi, ba wai karba irin ta zan karbi Haidar ba, a’a! irin yaro ya dan je hutu, da yake yakan zo ya dauke shi su tafi yawo to, daga irin haka ne aka tafi da shi yana da shekara biyu da wata daya aka karbe shi a hannuna, sai da na yi kusan wata shida ban ji muryarsa ba, ban sa shi a idona ba, sai ranar sunan dan’uwansa me bin sa, mahaifiyar yaron ta kira ni zan zo suna? Na ce zan zo dan lokacin azumi ne ana gobe sallah aka yi sunan kaninsa, bayan an sha ruwa sai na je sunan to, a ranar ne aka fara ba ni shi aka ce na tafi da shi, daga nan sai ya fara zuwa ‘weekend’ yana wajena, lokacin makaranta kuma yana can gidan babanshi sabida makaranta.
Rungumar dana ina da ‘right’ na rungumi dana na sumbaci dana, dana ne wanda na haifa da cikina babu wani abu na sha’awa tsakanina da dan da na haifa.
Ina rungumarsa ne ina jin dadi ‘because’ dana ne kuma ina son sa kuma shi kadai gare ni, dan yanzu shekararsa sha shida 16 kuma ba wai na kara aure ba ne na haihu, ba dan’uwa gare shi ba, shi kadai ne, ni kuma uwa ce me kawazucin danta, wannan rungumar da nake masa soyayya ce ta uwa da da, ko Ubangiji da kansa ya boye son da ke tsakanin Uwa da Da, wai ka gane girman soyayyar da ke tsakanin mahaifiya da abin da ta haifa kenan, to! ‘who are you’ a matsayinka na mutum ka zo ka yi ‘judging’ dina dan na rungumi dana?
Abin da na haifa abin da har na mutu ba zan taba sha’awarsa da wani abun banza ba, dan ni duk girman da yake da shi ganinsa nake kamar dan nan da na haifa dan jariri ne har yau, haka nake ganin shi, dan baby nake kiransa har yanzu, wani lokacin na ce masa Haidar amma na fi ce masa ‘Baby’ a kan Haidar, wannan mutane ne da nasu ‘misconception’ din da kuma tunanin banza, ‘but to me’, ni dai a matsayina na Uwa dan na yi bidiyo na soyayya ina rungumar yaro na kuma wakokin ma inda nake samu guri ne na tsananin soyayya irin wanda za ka iya yi wa iyayenka da suka haife ka sai abin da ka haifa su kadai za ka iya yi wa wannan ‘words’ din soyayyar ya dace, shi ya sa a daidai wannan wakar in na ga soyayyar ba soyayya ba ce na wani saurayi soyayya ce ta gaske wadda iyayenka su kadai za ka iya yi wa soyayyar wannan baitin nake hawa da dana na rungume shi, sabida ni na haifi abuna, da nake nakudarshi ina mutane suke?
Da nake laulayinshi wa ya san yadda na yi? Wa ya san rainon cikinsa da na yi ba tare da mahaifinsa ba yana rufe? Duk mutane ba su tunanin wannan kawai ‘Negatibity’ kawai tunaninsu na banza shi ne kawai suke magana a kai ba su duba ‘the other way around’. Eh!
Wasu sun yi magana kamar sun ban shawara a rayuwa yanzu ka-za ka-za ya lalace mutane ‘can use opportunity’, wasu na dauki ‘adbice’ dinsu amma ni dai a yadda na yi da zuciya daya na yi kuma zan yi shi sau millions idan ina so, dana ne ni na haifi dana ba wani ne ya haifa mun ba, ba kuma wani ne ya yi mun wahala da shi ba, ni na yi wahala da abuna.
Da yawan wasu mutanen suna ganin yawan ambaton tsohon mijinki da kike yi a soshiyal midiya yana nuni ne da son komawa gare shi, me za ki ce a kan hakan?
Da so nake na koma gidansa da na koma gidan tuntuni, da nayi aure, tunda tsakanina da shi sai idan na yi aure na fito kuma kullum ina fadar ba na fatan na yi aure na fito wai dan zan koma gidan tsohon mijina, ina son in na yi aure na yi na har abada kenan.
Ambaton tsohon mijina kamar abu ne wanda ‘I can’t help like’ Adamu ya zama ‘part of’ rayuwata ni ma na zama ‘part of’ rayuwarsa, yau Adamu in za a ce wace ce matarsa ta farko zai ce Amina, wace ce Uwar Haidar zai ce Amina. Idan zan ambace shi sai idan abun da ya shafi zan amba ce shi nake ambaton sa, ba wai haka kawai nake ambatonsa ba, a kan me haka kawai zan ambace shi?
Idan komawa nake so na yi ai da tuntuni na koma, ba wai ban da maneman ba ne ba, ba wai na rasa masu neman aure na ba ne akwai su da yawa, ina son na dauki lokacina ban so na yi abin da zan je na dawo, mace ce ni ba zan so a matsayina na mace ana kirga mun aure ba shi ya sa na dauki lokaci na har zuwa yanzu.
Ni ina so in na yi aure in sha Allahu na yi na har abada kenan, ambaton sunansa ba shi da wata alaka da son komawa gidansa, idan so nake na koma gidansa ai ana auren kashe wuta, mata dubu nawa suka yi; da tuni na yi auren kashe wutan na fito na dawo gidansa, amma yanzu kusan shekara nawa na rabu da shi tun Haidar na da wata biyar, yau shekara goma sha shida da tuntuni na yi wani auren na koma gidansa in dai ambaton sunanshi yana nufin ina son na koma gurinshi ne, wannan magana ce kawai irin ta mutane wacce ba za ka hana su yi ba su da bakinsu.
Kwanan baya Adam ya yi wasu maganganu da yake zargin ayyukan assha a tsakanin iyalansa har ta kai ga sakin aure, me za ki ce a kan hakan, musamman yadda ke ma ki ke daya daga cikin tsofaffin matansa?
Eh! to, a wannan dai ba abin da zan iya cewa dan bai shafe ni ba, duk abubuwan da ya yi ban da alaka da su ban san su ba, an bata masa rai ne abokan aikinsa ko wa ya taba shi? ya dai faffadi dai a ‘page’ din shi, ya yi maganganu sosai, duk da dai gaskiya ni ban wani bi ta kan abin ba ina ganin maganganun da aka fada mun kamar an yi masa asiri kawai ban shiga ‘social media’ ba ranar sai daga baya, na ga ana ta turo mun ana tagin dina sai nake tambayarsa me ya faru? ‘Because’ ban da matsala da shi, dan kafin ranar ana gobe abun zai faru ina ‘libe’ na je wasan sallah a Minna na yi ‘inbiting’ dinshi ya shigo fejina muka hadu muka yi hira a ‘libe’ dina aka yi wasa da dariya har wasu suka rika tunanin da ma haka muke yi?
A gaske mutanen gani suke idan muka ga juna kawai wuce juna muke yi mu yi tsaki, wai mutane ba su san yadda muke da Baban Haidar ba, rabuwa muka yi wanda kamar yadda ya fadi ya ce mata biyu a cikin matan da ya aura zai iya cewa ya yi da-ya-sanin rabuwa da su.
Daya zai ce yarinta, daya kuma abin da ta yi masa bai kai ya sake ta ba ya sake ta. Idan aka yi maganar yarinta ni da shi muka yi auren yarinta, lokacin yana jin kansa yana yaro lokacin, irin shekara 26 ne.
Dukkanin abubuwan da suka faru da shi ban san da shi ba, ba matsalata ba ce, bata masa rai aka yi ya fito ya nuna baccin ransa, kuma mun yi magana yake nuna mun abin da ake yi masa ne ya yi yawa, ya gaji, ka-za ka-za na dan ba shi iya shawarar da zan iya ba shi.
Dan daga farko ma ya sha ‘may be’ zan masa magana a kan maganganun da yake fadi matansa ka-za ka-za sunanmu da ya jero to, ina ma tambayarsa na ce me ke faruwa? ‘the nedt answer’ da na gani shi ne ya ce mun wannan abun bai shafe ni ba, ba da ni yake yi ba bai shafe ni ba, kawai an bata masa rai ne kuma ya gaji shi ya sa ya fito yayi magana, shi ne kawai abin da na sani.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa